Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-12 16:59:23    
Beijing da larduna da yankuna masu makwabtaka da ita za su hada gwiwa domin tabbatar da ingancin iska a lokacin gasar wasannin Olympic

cri
A kwanan baya, wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya sami labari daga hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin da cewa, birnin Beijing da birnin Tianjin da lardunan Hebei da Shanxi da Shandong da kuma jihar Mongolia ta Gida za su hada kansu wajen kyautata tsarin hadin gwiwa a tsakanin yankuna da kuma aiwatar da matakai daban daban domin tabbatar da ingancin iska a lokacin gasar wasannin Olympic.

An ce, yanzu hukumomin kiyaye muhalli na kasar Sin sun riga sun tsara matakai da dama wajen tabbatar da ingancin iska a lokacin gasar wasannin Olympic, a ciki har da kayyade kura a wuraren da ake yin ayyukan gine-gine, ,da rage kura a kan hanyoyi, da aiwatar da ma'auni a tsanake kan gas din da motoci suke fitarwa, da tsayawa tsayin daka kan takaita zirga-zirgar motoci a lokacin gasar wasannin Olympic, da kuma gudanar da shirye-shiryen hana gurbata muhalli a fannin masana'antu.(Tasallah)