Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-11 20:19:15    
Ko za a sassauta rikicin siyasa a Kenya ko a'a

cri

A kwanan baya, a lokacin da yake halartar wata jana'izar da aka yi domin wani dan majalisar kasar Kenya dan jam'iyyar 'yan hamayya, Raila Odinga, shugaban jam'iyyar 'yan hamayya ta Kenya wato ODM ya sake bukatar Mr. Kibaki, shugaban jam'iyyar hada kan al'umma ta Kenya, wadda ke mulkin kasar da ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kasar da kuma sake yin babban zabe. Wannan lamari ya murkushe kyautata zaton da aka yi a Kenya a kwanan baya, wato mai yiwuwa ne jam'iyyar da ke mulkin kasar da jam'iyyar 'yan hamayya za su cimma daidaito.

A ran 8 ga wata, a sakamakon shiga tsakani da Kofi Annan, tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da tawagarsa ta fitattun 'yan Afirka suka yi, Mr. Kibaki da Mr. Odinga sun yi shawarwari. Daga baya kafofin yada labaru na Kenya sun ba da labari cewa, wadannan jam'iyyu 2 sun sami ra'ayi daya kan kafa gwamnatin hadin gwiwa. Ko da yake Mr. Annan ya yi kira ga bangarori daban daban da kada su yi hasashe fiye da kima, amma ya bayyana cewa, lalle tattaunawa a tsakanin wadannan bangarori 2 ta cimma tudun dafawa. Ya kuma kara da cewa, mai yiwuwa ne jam'iyyun 2 za su cimma daidaito a mako mai zuwa. Bisa labarun da kafofin yada labaru na wurin suka bayar, an ce, bayan da suka yi shawarwari, jam'iyyar 'yan hamayya ba ta nace ga bukatar Mr. Kibaki da ya yi murabus ba, sa'an nan kuma, jam'iyyar da ke mulkin kasar ta yarda da yi tattaunawa da jam'iyyar 'yan hamayya kan abubuwan da ke shafar babban zabe, a maimakon bukatar 'yan hamayya da su kai kara a gaban kotu. An labarta cewa, bangarorin 2 za su sake yin tattaunawa a ran 11 ga wata domin tattaunawa kan kafa gwamnatin hadin gwiwa ta tsawon shekaru 2 ko 3, amma ba za su yi tattaunawa kan sake kidayar kuri'u ko kuma sake yin babban zabe ba.

Kafofin yada labaru sun tsamo kalami daga bakin majiya da cewa, bangarorin 2 da suka yi tattaunawa a tsakaninsu dukkansu sun yi sassauci, ta haka an shimfida hanya mai kyau wajen rarraba iko a tsakaninsu.

Amma duk da haka, jawabin da Mr. Odinga ya yi a gun jana'izar a ran 9 ga wata ya nuna cewa, jam'iyyar ODM ta canza ra'ayinta sosai. Manazarta sun nuna cewa, a lokacin da jam'iyyar ODM ta yin shawarwari da jam'iyyar da ke mulkin Kenya, Mr. Odinga ya fuskanci matsin lamba daga masu ra'ayin rikau na jam'iyyarsa, haka kuma, wasu 'yan jam'iyyar daga kananan hukumomi sun ki yarda da yin rangwame ga jam'iyyar da ke mulkin Kenya. Amma 'yan kallo sun bayyana cewa, yanzu ba a kwantar da kura a Kenya ba, mutane kimanin dubu 300 sun rasa wuraren kwana a sakamakon tarzomar da aka samu domin babban zaben. Ta haka da kyar za a sake kidayar kuri'u ko kuma sake yin babban zabe ba.

An labarta cewa, tawagar mashahurai ta Afirka za ta halarci wani taron musamman da sabuwar majalisar jama'ar Kenya za ta yi a lokacin hutu a ran 12 ga wata, inda za ta yi wa 'yan majalisar bayani kan ci gaban da aka samu a gun shawarwari a tsakanin bangarorin 2.

Manazarta sun yi nuni da cewa, tarzoma na tsawon fiye da wata guda da aka samu a sakamakon rikicin babban zaben shugaban kasar ta tono sarkakkan matsaloli da Kenya ke fuskanta a fannonin al'ummomi da gonaki da dai sauransu. Kuma da kyar manyan rukunonin siyasa da suke karawa da juna za su yi watsi da moriyarsu. Ran 9 ga wata, wata muhimmiyar jaridar wurin wato 'jaridar Tuta', wanda ke mara wa jam'iyyar 'yan hammaya baya, ta ba da misali da cewa, bangaren Odinga ya taba bayyana cewa, ya kamata a iya ganin matsayin da jam'iyyun majalisar jama'ar Kenya ke tsayawa a cikin gwamnatin hadin gwiwa ta wucin gadi. A cikin zaben 'yan majalisar jama'ar kasar da aka yi a shekarar bara a daidai lokacin da ake yin babban zaben shugaban kasar, jam'iyyar 'yan hamayya ta sami kujeru 99, amma jam'iyyar da ke mulkin kasar ta sami wasu 43 kawai. Shi ya sa mai yiwuwa ne jam'iyyar da ke mulkin kasar ba za ta yarda da kafa wata gwamnatin wucin gadi, wadda 'yan hamayya za su sami rinjaye.

Saboda haka Kenya tana bukatar karin lokaci domin fitar da kanta daga rikicin siyasa da take fuskanta a yanzu.(Tasallah)