Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-11 17:38:21    
Malam Woo Choon Kit, dan kasuwa na kasar Malasiya

cri

Malam Woo Choon Kit, dan kasar Malasiya wanda yake da shekaru 43 da haihuwa a bana, tun yake karami, yana sha'awar zuwa kasar Sin don ganam ma idonsa kasar Sin. A shekarar 1987 bayan da ya gama karatunsa daga wata jami'ar horon malamai ta kasar Malasiya, ya zo kasar Sin ya sami aiki. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, malam Woo Choon Kit ya riga ya shafe kimanin shekaru 20 yana aiki a birnin Tianjin da na Changchun da kuma Hong Kong da sauran wurare na kasar Sin.

Da Malam Woo Choon Kit ya tabo magana a kan aiki da zaman rayuwa da ya yi a kasar Sin, sai ya bayyana cewa, sabo da mahaifiyarsa Basiniya ce, shi ya sa ya saba da zaman rayuwarsa a kasar Sin cikin sauri. Birnin Tianjin birnin na farkjo ne da ya yi aiki a kasar Sin. Ya taba shafe shekaru 17 yana aiki a birnin. A shekarar 2005, Malam Hu Junjie ya tashi daga birnin Tianjin zuwa Hong Kong domin yin sabon aiki da aka ba shi. Da ya waiwayi abubuwan da ya ji a lokacin da ya tashi daga birnin Tianjin, sai ya ce, "a shekarar da na yi ban kwana da birnin Tianjin, ana raya birnin cikin sauri sosai, ana rushe tsofaffin gidaje cikin sauri, sa'an nan kuma ana yin sabbin gine-gine cikin sauri sosai. Na sami abokai masu arziki da yawa a birnin, sabo da haka na ji dadin zamanna sosai a birnin."

A shekarar 2006, an ciyar da malam Woo Choon Kit gaba, don ya zama babban manajan reshen babban kamfanin kera kayayyaki masu aiki da wutar lantarki na SMT a birnin Changchun da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Babban kamfanin SMT wani tsohon kamfani ne da ke samar da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki. Ba ma kawai yana aiwatar da harkokinsa a Hong Kong da sauran wuraren duniya daban daban ba, har ma ya dade yana samar wa kamfanin Seimens da na Sony da LG abubuwa masu inganci da ake bukata wajen harhada kayayyaki masu aiki da wutar lantarki. Birnin Changchun kuma muhimmin sansanin kera motoci ne a kasar Sin. Malam Woo Choon Kit ya ce, yau da shekaru da dama, babban kamfaninsa ya aika da ma'aikatansa zuwa birnin Changchun don yin bincike, kuma a shekarar 2005, ya hada kansa da babban kamfanin fasahar sadarwa mai suna Qiming na kasar Sin don kafa masana'antun kera kayayyakin wutar lantarki na motoci a birnin Changchun. Ya kara da cewa, "kamfaninmu na SMT ya fara yin bincike a yankin arewa maso gabashin kasar Sin ne a shekarar 2000, bayan haka yana fatan zai yi amfani da matsayi mai rinjaye da birnin ke tsayawa a fannin masana'antun kera motoci, wajen jawo kudin jari da fasaha don kafa masana'antun kera kayayyaki masu aiki da wutar lantarki a birnin."

Malam Woo Choon Kit ya ci gaba da cewa, babban dalilin da ya sa babban kamfaninsa ya zuba makudan kudaden jari wajen kafa irin wannan masana'antun kera kayayyakin wutar lantarki na motoci mai girma kamar haka a birnin Changchun tare da babban kamfanin Qiming, shi ne domin ana bunkasa sana'ar sadarwa cikin sauri sosai a kasar Sin. Malam Woo Choon Kit wanda ya shafe shekaru da yawa yana yin sana'ar sadarwa yana sa ran alheri sosai ga makomar raya sana'ar sadanarwa ta kasar Sin. Ya ce, "yanzu ana raya kimiyya da fasaha irin ta zamani a kasar Sin, kuma ana kara kokari wajen yin haka. Game da sana'ar sadarwa, mun fahimci sosai cewa, ma'aikatar sadarwa ta kasar Sin ta nuna babban goyon baya gare mu."

Bayan haka malam Woo Choon Kit ya ce, babban kamfani mai suna Qiming kamfani na farko ne da babban kamfaninsa ya hada kansa da shi a yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Ya kuma yi imani cewa, nan gaba kamfanonin da babban kamfaninsa zai hada kai da su kullum sai kara karuwa suke yi. (Halilu)