Bisa kalanda na gargajiya na kasar Sin, ran 7 ga wata a shekarar nan, sallar bazara ne na kasar Sin bisa al'adun gargajiya. A ganin mu sinawa, sallar bazara ta zama biki ne mafi muhimmanci a duk shekara, sabo da haka, a cikin lakacin sallar bazara, ko ina a kasar Sin ana yin bukukuwa irin daban daban don taya murnar sallar, akwai aikace-aikacen al'adun gargajiya da yawa ana ta yinsun har yanzu. A farko dai, muna fatan za ku saurari wata wakar mai suna "Maraba da zuwar sallar bazara", daga baya kuma, za mu yi dan bayani kan sallar bazara na kasar Sin. To, ga wakar:
Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara ita ce "Maraba da zuwar sallar bazara". Sallar bazara na kasar Sin ita ce rana ta farko ce na sabuwar shekara, an fara yin sallar nan don nuna ibada ga Ubangiji da kakakinmu a da da can. Da sallar bazara ta zo, mutane sun fara yin aikace-aikacen daban daban, don roki Ubangiji ya iya ba su kyakkyawar yanayi da kuma cikakken abinci a sabuwar shekar da ke zuwa. Game da sallar bazara, ana samu labaru masu ban sha'awa da yawa, cikin daya daga cikinsu, an ce, wani munafuncin dodo da aka kira "Nian" ya kan fita waje a karshen shekara, ya tafi kauyuka da birane, ya cinye mutane a can. Kakaninmu sun sha wahalar dodo nan sosai. Amma dodo nan ya ji tsaron marya da launin ja da hasken fitila, shi ya sa, da sallar bazara ya zo, kakakinmu su kan yi amfani da bindigar barazana da takardun musamman da aka manna kan gefunan kofa don isar da sakon alheri da fitila. Bayan shekaru da dama, wannan ya zama al'adun gargajiya na kasar Sin.
To, jama'a masu sauraru, yanzu kuma bari mu saurara wata waka mai suna "Muryar bindigar barazana ". Wakar nan ta bayyana farin ciki da sinawa suka ji lokacin da sinawa suka yi wasa da bindigar barazana. A cikin wakar, suna fatan ko wane iyali ya iya samu zaman klafiya da alheri da farin ciki a sabuwar shekara. Ga wakar:
Yanzu, irin abubuwan da sinawa suka yi don taya murnar sallar bazara su kara da yawa, sabo da canjawar zaman al'umma. Wadansu aikace-aikace masu jahilci kamarsu nuna ibada ga Ubangiji da dodo an riga an yi watsi da su yanzu, amma sauran aikace-aikace kamarsu manna kalmar "FU", da manna takardun musamman kan gefunan kofa don isar da sakon alheri, da shirya abincin gargajiya na Sin da aka kiransa Niangao da Jiaozi, da jiran sabuwar shekara ta zo, da kuma ziyara abokai don tayar murnar sabuwar shekara da dai sauransu har yanzu ana ta yinsu sabo da suna da ban sha'awa sosai. Yanzu za mu sanya muku wata wakar mai suna "Wakar kalmar FU" da mata da maza su rera tare don nuna muku fatan alheri. To, ga wakar:
Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara ita ce Wakar kalmar FU. A cikin wakar, an ce:"Kai kana son sa'a, ni ma ina son sa'a, sai a rera wata wakar mai suna Wakar kalmar FU don nuna dukkan mu fatan alheri. "
A cikin lokacin sallar bazara, bisa al'adun gargajiya na Sin, ko wani iyali za su share dakunansu za su manna hotunan gargajiya da aka kiransu Nianhua a cikin dakuna, ban da wannan kuma, za su manna takardun musamman masu launin jar a kan gefunan kofa don isar da sakon alheri, ko ina ana ganin yanayin sallar bazara. Wakar mai suna "Manna takardun musamman kan gefunan kofa don isar da sakon alheri" da wata mata ta rera ta bayyana farin cikin da sinawa sun ji lokacin da suka manna takardun musamman kan gefunan kofa. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu sanya muku wakar nan. Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara ita ce "Manna takardun musamman kan gefunan kofa don isar da sakon alheri".
Sallar bazara wata salla ce da dukkan membobin iyali za su taro, wannan ya yi kamar da bikin kirsimati na kasashen Turai. Yara da su fita daga iyali ya kamata su koma gida a jajibirin sabuwar shekara da dare, wato rana kafin sallar bazara. Sai dukkan membobin iyali su taro su ci abinci tare, abinci nan aka kiransa Tuanyuanfan ko Nianyefan. Bayan cin abinci, sai dukkan iyali suka zaune suka kewaye, suka yi hira game da abubuwan irin daban daban. Jama'a masu saunraro, yanzu kuma za mu saurara wata wakar mai suna "Tuanyuanfan" da wani maza ya rera.
A cikin wakar, an ce, a ci abincin da aka kira "Tuanyuanfan" a jajibirin sabuwar shekara da dare, dukkan membobin iyali, ko yara kanana ko tsohuwa su ji farin ciki sosai. Ana fatan tsohuwa suna da alheri kuma yara su samu nasara, kuma ana fatan masoyayya su iya zaman tare har abada da kuma dukkan iyali su yi zaman rayuwa mai jituwa. To, jama'a masu sauraro, yanzu bari mu saurara wakar nan, wato wakar mai suna "Tuanyuanfan", ga wakar:
A jajibirin sabuwar shekara da dare, mutane da ke arewancin kasar Sin su kan ci wani abinci da aka kira Jiaozi. A cikin wakar mai suna "Shirya Jiaozi a jajibirin sabuwar shekara da dare", wanda wata mata ta rera, ta bayyana farin ciki da dukkan iyali suka ji lokacin da suka taro suka shirya Jiaozi da kuma ci Jiaozi a jajibirin sabuwar shekara da dare. Ga wakar:
Bayan jajibirin sabuwar shekara ya gama, sai sabuwar shekara ta zo. A rana ta farko na sabuwar shekara, bisa al'adun gargajiya, sinawa su kan ziyara abokansu da yi gaisuwa sabo da sabuwar shekara ta zo. Ran nan da sassafe, kowa ya sanya kyakkyawar tufafi. Su tafi gidajen abokansu don gaisuwa, ko yi maraba da bako a gidajensu. Da mutane su gane juna, sai su yi gaisuwa su ce "Barka da sabuwar shekara!" ko "Fatan alheri!" da dai sauransu. Yanzu, bari mu sanya muku wata wakar mai suna "Wakar gaisuwa a sabuwar shekara", wanda ta bayyana abin da aka fada lokacin da aka yi gaisuwa a sabuwar shekara. To, ga wakar:
Kwanakin 15 bayan sallar bazara, wato ran 15 ga watan farko na sabuwar shekara, shi ne bikin Yuanxiao bisa al'adun gargajiya na Sin, ko ma iya ce bikin fitila. A ran nan da dare, mutane su kan fita waje, su kallon kyakkyawar fitilu irin daban daban da ke kan tituna. Wakar "Kallon kyakkyawar fitilu irin daban daban" ta bayyana halin da ke ciki a bikin Yuanxiao. Ga wakar:
Bayan bikin Yuanxiao, dukkan lokacin sallar bazara ya gama. To, jama'a masu sauraro, sai ku dan shakata kadan, daga bisani kuma za mu dawo domin kara sanya muku wasu wake-wake da Mr. Yu Yong ya rera. Mr. Yu Yong, dan kabilar Chaoxian ne, yanzu ya zama malam a kwalejin koyon ilmin kide-kide na kasar Sin. Ya tsaya wake-wake da kide-kide da yawa, yawan daga cikinsu su samu lambar kyauta a gasar wake-wake da kide-kide a ciki da waje. To, jama'a masu sauraro, yanzu kuma za mu sanya muku wata wakar mai suna "Fatan alheri ga mamata", wanda Mr. Yu Yong ya tsaya. Ga wakar:
|