|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-02-09 20:14:04
|
Za a dauki matakan tabbatar da kwanciyar hankali a cikin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa na birnin Beijing
cri
Bisa shirin da birnin Beijing ya tsara, za a dauki matakan tabbatar da kwanciyar hankali a cikin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa kafin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a karo na 29 a nan Beijing.
An labarta cewa, za a yi amfani da ma'aikata da injuna da karnuka wajen binciken fasinjoji. A cikin 'yan kwanakin nan, birnin Beijing ya riga ya soma aiwatar da wannan manufa a cikin wasu tashoshin jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa domin hana shigar da kayayyakin da za su fasa ko za su samu wuta da sauki a cikin jiragen kasa. (Sanusi Chen)
|
|
|