Lokacin da ake murnar bikin bazara na gargajiya na kasar Sin, jama'a masu fama da bala'in kankara mai laushi na yankunan kudancin kasar sun kuma shirya bukukuwan al'adu iri iri domin taya murnar bikin kamar yadda ya kamata.
A birnin Chenzhou da ya yi fama da bala'in mafi tsanani, daruruwan jama'a sun sanya tufafi masu launi iri iri sun taka raye-raye da ganga domin murnar bikin bazara. A waje daya kuma, wasu kungiyoyin wakoki da raye-raye sun nuna wa jama'a shirye-shiryensu a kan tituna.
Haka kuma, a lardin Guangdong, 'yan ci rani wadanda aka tsayar da su a birnin Guangzhou sun taya murnar bikin bazara ba kamar yadda suka taya murnar bikin bazara a garinsu ba, sun yi yawon shakatawa a lambunan shan iska. (Sanusi Chen)
|