Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-08 19:51:47    
Yaya Sinawa suke kirga shekaru da sunayen dabbobi

cri

Masu karatu, bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, tun jiya ne muka shiga wata sabuwar shekara, wato shekarar bera, sabo da haka, muna taya dukan masu sauraronmu murnar shiga sabuwar shekara ta Sinawa. Da jin abin da na fada, watakila akwai masu sauraronmu da ke tambaya, "mene ne shekarar bera?", to sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, za mu amsa wata tambaya dangane da al'adar Sinawa ta yin amfani da dabbobi wajen kirga shekaru, kuma tambayar da za mu amsa ta zo ne daga hannun malam Isa salihu, wanda ya fito daga birnin Ikko, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana, malam Isa ya ce, shin gaskiya ne Sinawa suke amfani da sunayen dabbobi wajen kirga shekaru, kuma yaya suke yi?

Masu karatu, Sinawa su kan kirga shekaru ne da dabbobi 12, wato ban da bera, akwai sauran dabbobi 11, ciki har da sa da damisa da zomo da dragon da maciji da doki da rago da biri da kaji da dai sauransu.

Tun tuni a karni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, Sinawa sun fara yin amfani da dabbobi 12 wajen kirga shekaru, kuma ya zuwa karni na 5 zuwa na 6, al'adar ta riga ta zama ruwan dare. Bayan kirga shekaru, kakan kakanin Sinawa sun kuma yi amfani da dabbobin 12 wajen kirga watanni da kuma lokuta na kowace rana.

Bayan haka, kakan kakanin Sinawa su kan hada dabbobi biyu biyu a gu daya, wadanda suka bayyana burinsu. Sabo da suna ganin cewa, Bera na da hikima, kuma shanu na da kwazo, kuma wadanda ke da hikima idan ba su yi kokarin aiki ba, sun zama masu wayo kawai. Amma wadanda ke kokarin aiki idan ba su yi hankali, shashasha ne, sabo da haka ne, dole ne a hada halayen biyu. Sa'an nan, sun kuma hada damisa da zomo a gu daya, sabo da damisa na da jarumtaka, kuma zomo yana taka tsantsan. Dole ne a hada halayen biyu a gu daya, sabo da ba za a iya cimma nasara ba sai dai an sami jaruntaka tare kuma hankali.

Game da me ya sa kakanin kakanin Sinawa su kan kirga shekaru da sunayen dabbobi, dalili shi ne sabo da ilminsu na taurari. A zamanin da, kakanin kakanin Sinawa sun gano cewa, lokacin zafi da lokacin hunturu suna canzawa, kuma wata ya kan cika har sau 12 cikin shekara guda, sabo da haka, sun tsai da dabbobi 12 wajen kirga shekaru.

Bayan haka, a cikin jerin wadannan dabbobi 12 da ake amfani da su wajen kirga shekaru, an jera bera a farko, to, watakila akwai masu karatun da ke da tambaya, "me ya sa aka jera karamar bera a farko?" Game da tambayar, wasu suna ganin cewa, dalili shi ne a farkon kowace rana, bera ta fi aiki. Bayan haka, akwai kuma wasu tatsuniyoyi da ke barbazuwa a kasar Sin game da yadda aka jera wadannan dabbobi 12.

An ce, a da da da can, ubangiji ya kira dabbobin duniya, don zaben dabbobi 12 da za a kirga shekaru da su. Bayan da aka watsa labaru, sai dabbobi suka yi murna sosai, kowanensu ya je wurin taro cikin gaggawa, don kada a bar shi a baya. Amma kashegari, lokacin da bera ya isa fadar ubangiji, sai ta tarar da cewa, kai kowa ya riga ta isa. Saniya ta tashi tun jajiberen sabuwar shekara, shi ya sa ta zo ta farko, kuma damisa ta zo ta biyu, bayanta sai zomo da dragon da maciji da doki da rago da dai sauransu, wato bera ta zo ta karshe ke nan.

Sai kuma a lokacin da za a jera dabbobin, ubangiji ya yi tunanin cewa, ko da yake saniya ba ta da wayo, amma ga girmarta da kuma karfinta, ga shi kuma ta zo ta farko, shi ya sa ya yanke shawarar jera shi a farko. Ga shi kuma bera karama ce, kuma ta zo ta karshe, ba shakka ya kamata a jera ta a karshe. Amma da zarar ubangiji ya fara magana, sai bera ta yi tsalle a gabansa, ta ce, "zancen girma ba zai iya wuce ni ba. In ba a gaskata ba, bari jama'a su yanke shawara." Maganar bera ta ba ubangiji dariya, amma duk da haka, ya yarda, ya umurci dabbobin su je titi.

Lokacin da saniya ta fito a kan titi, jama'a suna fara'a, sun nuna yabo a gare ta, amma ba wanda ya ce tana da girma. A lokacin, ba zato ba tsammani, bera ta dare kan saniya, har ta tsoratar da jama'a, sun ce, "kai, daga ina ne aka fito da bera mai girma haka?" To, shi ke nan, ba yadda za a yi sai ubangiji ya jera bera a farko.(Lubabatu)