Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-08 19:42:37    
Bayani kan gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yanzu

cri

Jama'a masu sauraronmu, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a zaurenmu na " Wasannin Olympic na Beijing". Yau dai, muna so mu gabatar muku da wani labari na game da wasannin Olympics. Yanzu, sai ku gyara zama don ku saurari wani bayani kan gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yanzu.

A maraicen ran 6 ga watan Afrilu na shekarar 1896 da misalin karfe 3, Sarki Johann Georg 1 na kasar Girka ya yi shelar bude gasar wasannin Olympic ta farko a wancan zamani. Mr. Pierre Coubertin da kuma sauran manyan jami'an kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa sun halarci bikin bude gagarumar gasar, inda aka buga wani kida mai kayatarwa, wanda kwamitin wasannin Olympics na duniya ya mayar da shi a matsayin taken gasar wasannin Olympics a shekarar 1958. Mai tsara kidan taken shi ne Mr. Spiros Samaras na kasar Girka; kuma mai rubuta kalmomin taken shi ne Mr. Costis Palamas. Lallai 'yan kasar Girka sun nuna himma sosai ga wannan gagarumar gasar. 'Yan kallon da suka halarci bikin bude gasar sun kai kimanin dubu tamanin.

Jama'a masu sauraro, da yake akasarin kasashen duniya sun samu ilmi kadan a fannin gasar wasannin Olympic ta farko a wancan lokaci, shi ya sa kasashe kalilan ne suka mayar da martani kan goron gayyatar da kwamitin shirya gasar ya yi wa kasashe da dama. An labarta cewa, kasashen Amurka, da Jamus, da Faransa da kuma Denmark da dai sauran kasashe 9 tare da 'yan wasa maza 241 kawai sun shiga gasar din.

An shirya manyan ayyukan wasanni iri 9 da kuma kananan ayyukan wasanni iri 43 a gun gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yau, wadanda suka hada da wasan guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan sukuwar keken hawa, da wasan ninkaya, da wasan lankwashe jiki wato Gymnestics, da wasan kokawa, da wasan kwallon tennis, da wasan takobi, da wasan daga nauyin karafa da kuma wasan harba kibiya da dai sauransu. Bisa yadda aka saba yi a gun wasannin Olympics na can can zamanin da, ba a shirya wasanni na kungiya-kungiya da kuma gasanni na mata ba a gun gasar wasannin Olympics ta farko a zamanin yau.

Gasa ta farko ta wasannin Olympics na karo na farko a zamanin yau, an gudanar da ita ce kan filin wasan guje-guje da tsalle-tsalle, inda aka taba yin gasar wasan takobi lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics na Aden a shekarar 2004. Wannan filin wasa na iya daukar 'yan kallo da yawansu ya kai 60,000, wanda shi ne mafi girma a duniya kafin shekarar 1932.

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, zakaran farko a tarihin wasannin Olympics na zamanin yau, shi ne dan wasa mai suna James Connolly daga kasar Amurka, wanda ya zo na daya a gun gasar tsallen nesa na yin dira 3 da tsawon mita 13 da digo 71 ; Amma abun bakin ciki shi ne, Jami'ar da yake yin karatu a can ta kore shi daga Jami'ar yayin da yake koma wa kasa tare da lambar zinariya ta wasannin Olympics domin kuwa shi Connolly wanda ya kasance wani dalibi na aji na biyu na Jami'ar din a wancan lokacin bai samu izinin zuwan kasar Girka don shiga gasa ba. ( Sani Wang )