Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-08 18:07:22    
Gwamnatin kasar Chadi ta riga ta sarrafa halin da kasar ke ciki

cri
A ran 7 ga wata, an kara sassauta halin da kasar Chadi ke ciki. Domin taimaka wa wasu yankunan kasar wajen kwantar da kurar da aka tayar tun da wuri da kuma daidaita hasarorin da aka samu sakamakon yakin da aka tayar, a ranar, firayim ministan kasar Chadi Nouradine Coumakoye ya sanar da cewa, za a aiwatar da dokar hana fitar dare a birnin N'Djamena, babban birnin kasar da kuma sauran yankuna shida da ke tsakiya da kuma gabashin kasar. Kuma za a kaddamar da dokar tun ranar da aka sanar da ita. Za a hana fita waje daga karfe 6 da rabi da dare zuwa karfe 6 da safe a ko wace rana.

Sojojin gwamnatin Chadi da dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin sun yi musanyar wuta mai zafi a wurare da ke kusa da birnin N'Djamena daga ran 1 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki. Har ma dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin sun taba shiga birnin N'Djamena da kuma kewaye fadar shugaban kasar Chadi. Bayan musanyar wuta mai zafi da aka yi a kwanaki da dama, a ran 6 ga wata, gwamnatin kasar Chadi ta sanar da cewa, sojojin gwamnatin sun riga sun sake mallakar birnin N'Djamena da kuma halin da duk fadin kasar ke ciki.

Bayan da dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar Chadi suka janye jiki daga birnin N'Djamena a ran 3 ga wata, sun taba sanar da cewa, suna zama a kusa da birnin, kuma watakila za su sake kai farmaki a ko wane lokaci. Amma har zuwa ran 7 ga wata da dare, ba a samu sabon farmaki ba. A ran 6 ga wata da yamma, shugaba Idriss Deby na kasar Chadi da ministan tsaron kasar Faransa Herve Morin da ya yi ziyara a kasar sun shirya taron manema labarai tare a fadar shugaban kasar, inda ya sanar da cewa, sojojin gwamnatin kasar Chadi sun riga sun soma sarrafa halin da duk fadin kasar ke ciki. Shugaba Deby ya kara da cewa, sojojin gwamnatin sun lashe dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kwata kwata.

Hukumomin samar da taimako sun kiyasta cewa, 'yan kasar Chadi kusan dubu 60 sun gudu zuwa kudu, wasu kuma sun shiga kasar Camerron da ke makwabtaka da kasar Chadi. Tare da kwararowar 'yan gudun hijira, an fara samun karancin kayayyaki a gundumar Kousseri da ke arewacin kasar Cameroon, farashin abinci da kuma ruwan sha ya samu karuwa sosai, kuma dimbin 'yan gudun hiriji sun bayyana cewa, ba su iya daure wannan nauyin da ke bisa wuyansu ba. Bisa bukatun da bangaren 'yan sanda na kasar Chadi ya yi, darurruwan 'yan gudun hijira sun riga sun koma wa birnin N'Djamena. Amma yawancinsu suna jin tsoron koma gida sakamakon damuwa da farmakin da dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin Chadi za su tayar.

Kungiyar tarayyar Turai wato EU ta taba tsara shirin aikawa da sojojin kiyaye zaman lafiya 3700 zuwa kasar Chadi a farkon watan Fabrairu domin kare 'yan gudun hijira dubu darurruwa da aka tsayar da su a gabashin kasar Chadi, da kuma samar da taimako wajen gudanar da aikin agaji na jin kai a shiyyar Darfur ta kasar Sudan. Amma a karshen watan Janairu, halin da kasar Chadi ke ciki ya tsananta ba zato ba tsammani, shi ya sa kungiyar EU ta dakatar da shirin jibge sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar.

A ran 7 ga wata da safe, shugaba Deby na kasar Chadi ya yi kira ga kungiyar EU da ta jibge sojojin kiyaye zaman lafiya a kasashen Chadi da Afirka ta Tsakiya tun da wuri. Kuma an labarta cewa, yanzu wannan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da ake iya samun sojojin kasar Faransa mafi yawa a ciki ta riga ta samu amincewa daga MDD da kuma gayyatar da gwamnatin kasar Chadi ta yi mata, watakila za a tura su zuwa Chadi a cikin gajeren lokaci. Manazarta suna ganin cewa, idan sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar EU suka shiga yankunan da ke gabashin kasar Chadi, to mai yiyuwa ne dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin za su nemi sulhu da gwamnatin, ta haka ana sa ran cewa, sannu a hankali za a kwantar da kurar da aka tayar a kasar.(Kande Gao)