Ran 7 ga wata, ranar bikin Bazara a gargajiyar kasar Sin. Ko da yake a kwanakin baya, an samu bala'in kankara mai laushi da kuma kankara a kudancin kasar Sin, amma jama'ar al'ummomi dabam daban suna taya murnar bikin Bazara ta hanyar yin bukukkuwa masu kayatarma.
A wannan rana a nan birnin Beijing, ana cikin yanayin murnar bikin Bazara ko ina, bukukkuwan wasannin nihsadi na gargajiya fiye da 20 sun jawo hankulan dubban mazauna. Ba kamar bukukkuwan da aka yi a da ba, bukukkuwa na shekarar da muke ciki suna da yanayin wasannin Olympic da salon wasannin Olympic kwarai.
A birnin Guangzhou, an yi rana sosai. Manoma 'yan ci rani wadanda ba su koma gida ba saboda bala'in kankara mai laushi suna murnar bikin Bazara amma ba irin yadda ake yi a gida ba. A birnin Chenzhou na lardin Hu'nan inda aka taba samun bala'in kankara, ana jin farin ciki a lokacin bikin Bazara saboda gwamnatoci dabam daban sun yi iyakacin kokari domin ba da tabbaci wajen samar da abin masarufi.
A ran 7 ga wata, a sa'i daya mutane fiye da miliyan 2.8 na lardin Tibet sun yi maraba da bikin Bazara da sabuwar shekara bisa kalandar Tibet.
|