Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-07 21:15:23    
Dan Korea ta kudu ya ba da taimakonsa ga yara kanana na kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya ruwaito mana kan wani dan Korea ta kudu wanda ya ke zama a birnin Tianjin da ke arewancin kasar Sin kuma ya samu kauna da girmamawa daga mutanen wurin. Bayan da ya zo nan kasar Sin a shekara ta 2003 ya kafa wata masana'anta kuma ya ba da taimakon kudi ga marayu 13 dake fama da talauci,ta haka wadannan marayun za su iya kammala karatunsu. Bisa taimakon da ya bayar, aka baiwa masa sunar mazaunin birnin Tianjin mai daukaka,aka kuma zabe shi da ya zama daya daga cikin nagartattun mazauna goma na birnin Tianjin

A ran 10 ga watan Nuwanba na shekara ta 2006 a dakin daukar hotuna na gidan telebiji na birnin Tianjin, an mika wata takardar shaidar nagartaccen mazaunin birnin Tianjin ga wannan dan Korea ta kudu mai suna Kim Yeong Rea. A cikin zaben da mazaunan birnin miliyan daya da rabi suka shiga, Kim Yeong Rea shi ne bako daya kawai aka zabe shi da ya zama nagartaccen mazaunin birnin Tianjin. Wannan dan kasuwa na Korea ta kudu ya nuna kauna ga yara kanana na kasar Sin,ya ba da taimakon kudi ga yaran dake fama da talauci wajen ci gaba da karatunsu,aikin da ya yi tare da kauna ya girgiza mutanen birnin Tianjin. Yayin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya yi hira da shi,Mr Kim Yeong Rea ba ya so ya bayyana abubuwa masu kirkin da ya yi ba. Ya ce, " Kamata ya yi a ba da taimako ba tare da son zuciya ba, bai kamata a gaya saura taimakon da ka bayar ba. Mazaunan yankin Beicheng na birnin Tianjin sun yada labari dangane da aikin da na yi, mutanen da suka sane da ni sai kara yawa suke, ba na ji dadi sosai da ganin haka."

Mr Kim Yeong rea wani manaja ne na wani kamfanin kera kayayyakin electronics.A shekara ta 2001 ne ya zo birnin Tianjin domin kafa masana'anta. Yayin da yake kokarin kafa masana'anta, ya ga wasu marayu ba su samu damar shiga makaranta ba saboda talauci,wasunsu ba su iya rubuta sunayensu ba. Mr Kim Yeong rea ya yi bakin ciki da ganin haka, ya kuduri aniyar ba da taimako ga wadannan yaran. A shekara ta 2004, ta gwamnatin wuri ya zabi marayu yara kanana 13 da suke kasancewa cikin talauci suka gaza ci gaba da karatunsu,ya ba da taimakon kudin Sin Yuan dari uku ko wane wata ga kowanensu. Kuma ya kan gayyace su da su je kamfaninsa ya ci abinci tare da su cikin lokaci lokaci,ya tambaye su yadda suka yi zama da karatu,ya kuma fadakar da kansu ta yadda za su girma cikin lami lafiya

A hakika, Mr Kim Yeong rea ya ba da taimako ga matasa dake fama da talauci a kasar Korea ta kudu cikin shekaru 15 da suka shige kafin ya zo nan kasar Sin.Me ya sa ya ci gaba da ba da taimako bayan da ya zo nan kasar Sin. Mr Kim Yeong rea ya ce ban da amincin da tausayin da mazaunan birnin Tianjin suke nunawa marayu yara kanana,gwamnatin wuri ta birnin Tianjin ta ba da nata taimako a kai.

"Kamfanin Bosta (kamfani ne da Mr Kim Yeong Rea ya kafa) ya shafe shekaru da dama tun kafuwarsa.A lokacin da aka kafa kamfanin, gwamnatin Beichen na birnin Tianjin ya ba ni,dan kasuwa na Korea ta kudu,taimako mai tarin yawa.in babu taimakonsu babu kamfaninsa. Abin da na ke tuna a yanzu shi ne ya kamata in yi wani abu domin mayar da martani ga gwamnatin wurin,sai na ba da taimako nawa ga wadannan yara kanana."

Tare da taimakon da Mr Kim Yeong Rea ya bayar,wadanan yara kanana 13 ba ma kawai su ci gaba da karatunsu, har ma sun sami tarbiyya mai nagarta, sun girma tare da koshin lafiya da tunanin kirki.A karo na farko da Mr Kim Yeong rea ya gana da yara kanana 13 a cikin ofishinsa,wata yarinya ta boye kanta a bayan saura ta yi shiru ba ta so ta yi magana. Bayan da aka bi diddigin, ya sane da cewa iyayen yarinyar sun rasu, ta samu matsin lamba wajen tunani da zama,shi ya sa ta kan jin gazawa ta kan shiga kadaici,ba ta so magana, ko ma a cikin ajin daukar darasi ,duk da haka ba ta samu cigaba sosai ba a cikin karatu. Da ganin haka, Mr Kim Yeong rea ya gane da cewa talauci da kadaici sun kawo mugun tasiri ga yaran wajen tunani. Sai ya yi hira da yarinyar, ya yi mata kwarin gwiwa da ta kalubalanci zama da jar zuciya, ya yi mu'amala da kakaninta, bisa sha'awar da yarinyar ta nuna, ya yi mata rajista a wani kos na koyon raye raye, ya kuma je wurin koyon raye raye ya dudduba yadda take koyo da karfafa zuciyarta. Daga baya yarinyar ta nuna fara'a a kai a kai,kuma ta samu ci gaba sosai wajen karatu.

A rakiyar Mr Kim Yeong rea,wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya zo makarantar da wannan yarinya mai suna Ma Yuqin ke kartu a ciki domin nuna mata fatan alheri.Ma Yuqin tana cikin aji na shida na makarantar firamare, ta samu ci gaba sosai wajen karatunta. Da ta ga Mr Kim Yeong rea tare da wakilinmu,ta mika gaisuwa,ba a iya gano wani kadaici da gazawa daga wajenta ba. Da aka juya magana kan Mr Kim Yeong Rea, cike da fara'a, Ma Yuqin ta bayyana cewa "ko wane wata na je kamfanin kaka Kim sau daya, kaka Kim ya ci abinci tare da mu, ya ba ni kudin Sin Yuan dari uku kowane wata na zama. Kamata in yi kokarin karatu, in mayar da martani zuwa gare shi da abubuwa masu kirki."

Wata yarinya mai suna Zheng rong da Mr Kim Yeong rea ta ba ta taimako tana karatu a aji na uku na karamar makarantar middle.Uwarta ta rasu yayin da ta haife ta, ubanta ya kashe kansa sabo da tsananin ciwon da ya yi fama da shi, ba wanda ya kula da ita sai kakaninta masu fama da cututtuka. Ta yaya wannan yayinya ta jure wannan wahalar da ke gabanta.Yarinya Zheng Rong dake fama da wahala ta yi sa'a ta gamu da Mr Kim Yeon rea. Mr Kim ya nuna mata aminci, ya kubutar da ita daga mawuyancin hali. Zheng Rong ta ce daga wajen Mr Kim Yeong rea na koyi yadda zan ba da taimakona ga sauran yayin da suke kamu da wahala. Kan makomarta yarinyar ta ce tana so ta zama irin mutum kamar Mr Kin Yeong rea wanda ya ka ba da taimako ga saura.

" Na taba yi tsammanin bude wani kamafani da na girma,in ba da taimako ga daliban da ke fama da talauci. idan na gaza samun aikin yi,zan iya aiki a kamfanin nan." Malama mai koyarwa Liu Xinghong wadda take kula da ajin da Zheng Rong ke ciki ta ga yadda Zheng Rong ta girma ta bayyana cewa

"Wannan yarinyar ba ta yi kamar sauran yara ba saboda ta rasa kaunar iyayenta tun tana karama.Na taba hira da irin wannan yarinyar,su kan jin karaya a cikin zamansu a ganinsu suna cikin duhu, babu kauna babu fara'a. Bayan da Mr Kim Yeong Rea ya ba su taimako, tana jin kauna a ko ina a zamantakewa, kuma mutane da yawa suna taimakonta,ta ce kamar ta sake samun gida tana jin dadin zama. Bayan haka ta fara nuna fara'a, ta kuma nuna kwazo da himma wajen mu'amala da 'yan makaranta,ta sa kulawa ga ajin da take ciki da ba da taimako ga 'yan ajinta."

Bisa tasirin Mr Kim Yeong rea,matarsa ta zama magoyi bayan wadannan yara kanana marayu. Da ta shirya abinci mai kyau, ta kuma shirya wasu dominsu, da ta je kasuwa ta saye tufafi, ita ma ta saye domin yaran.'ya'yansu biyu daya da yake karatu, dayan diya da take aiki a birnin Tianjin su ma sun dauki wadannan marayu kanana kamar 'yanuwansu, su kan kula da karatunsu. Ga shi yanzu suna zama cikin babban iyali suna jin dadin zaman tare cikin lumana da kwanciyar hankali. Haka kuma bisa tasirin Mr Kim Yeong rea,ma'aikatan kamfaninsa ma suna nuna kauna ga wadannan yara suna so su taimake su. Ma'aikacciya Gong Nina ta wannan kamfanin tana so ta yi mu'amala da yaran, ta dauki kanta a matsayin 'yar wadannan yara kanana.Gong Nina ta ce, "aikin da manajan kamfaninmu Kim Yeong rea ya yi a matsayin bako na kasar Sin ya girgiza ni kwarai da gaske,ya nuna halin kirki ga yara kanana na kasar Sin, ya kamata in yi koyi da shi. Ko da ya ke ni ba ni da karfi kamar shi wanda ya ba da kudin taimako ga yara, zan iya yin hakan bayan zan sami isashen kudi." Duk lokacin da aka tabo batun samar da taimakon kudi ga yaran, mr Kim Yeong rea ya yi murmushi. Ya ce abin alheri gare shi da ya ga wadanda marayu kanana da suka samu taimakona suna zaman jin dadi da cike da kyakkyawan fata ga makomarsu a nan gaba.

" Da na ga wadannan marayu kanana 13 a karo na farko, babu alamun murmushi a fuskokinsu,wata kuma tana so ta boye kanta yayin da ta ga bako,ga shi a yau suna dariya, suna jin dadin zama, na ga suna girma yadda ya kamata, ina alfahari."

Mr Kim Yeong rea ya ce da farko na tsai da kudurin ba da taimakon kudi ga yara kanana 13,dalili kuwa shi ne kamfanina na da ma'aikata 13 kawai a wannan lokaci ciki har da ni. ga shi a yau, daga cikin yaran da suka samu taimako daga wajen ni,wasun su sun girma sun kai shekaru 18 da haihuwa,wani kuma ya shiga muhimmiyar jam'ia ta gwamnati ta hanyar jarrabawa,yanzu ina shirin samarwa wasu yaran da suka girma yanci da su ci gashin kansu. Ina shirin kara yaran da suka samu taimako daga wajenna da su kai talatin a wannan shekara, in na sami dama ina so in gina wani ginin kwana domin su ta yadda za su iya cin abinci da kwana tare,su taimaki juna kuma za su samu ci gaba tare.

Jama'a masu sauraro,wannan shi ya kawo karshen shirinmu na zaman rayuwar sinawa. To lokacin shirinmu ya kure,mun gode muku saboda kun saurarenmu sai wannan lokaci a mako mai zuwa.(Ali)