Kamar yadda kowa ya sani,kasar Sin tana da dogon tarihi,yankinta yana da fadi kwarai da gaske.A fannin al`adar daure aure,tun can can da har zuwa yanzu,al`adar daura aure ta kasar Sin tana yin sauye-sauye,amma,halin da ake kago a wurin bikin daura aure wato gagarumi da farin ciki bai canja ba ko kadan.***
A zamanin da,al`adar daura aure ta kasar Sin tana da ban sha`awa.Idan wani saurayi yana son wata budurwa,sai dole ne ya gayyaci wata waliyiya saboda ta je gidan budurwa domin yin rokon daura aure.A wannan lokaci,ba ma kawai iyayen saurayi su bai wa waliyiya kyauta ba,har ma dole ne su bai wa iyayen budurwa kyauta.Waliyiya ta je gidan budurwa tare da kyauta,idan iyayen saurayi da budurwa sun yarda,to,za su kafa huldar dangin aure ta hanyar kira liyafa.Kodayake ba su kafa irin wannan hulda ta hanyar doka ba,amma tana da amfanin doka,wato bai kamata ba su canja irin wannan hulda kamar yadda suke so.A birnin Wenzhou na lardin Zhejiang dake kudancin kasar Sin,mutane su kan mayar da zobe a matsayin kyautar daura aure,a hakika dai,mutanen duk fadin duniya suna mayar da zobe a matsayin kyautar daura aure,saboda ma`anar zobe ita ce `har abada`,wato idan ango ya bai wa amariya zobe,to,wannan ya nuna mana cewar,ango da amariya za su yin zaman rayuwa tare har abada kuam za su jin dadinsu tare.
Bayan wannan,sai bikin yin aure,bikin ya yi gagarumi kwarai da gaske,kuma halin bikin yana da farin ciki sosai. A ranar da ake yin bikin daura aure,kullum amariya ta sa tufafi mai launin ja,nufinsa shi ne don nuna sa`a da farin ciki.Kafin amariya ta tashi daga gidanta,dole ne ta yi kuka,ma`anar wannan al`ada ita ce amariya ba ta so ta bar gidanta ba.Bayan amariya ta sauka a gidan ango,to,bikin daura aure ya fara.A wasu wurare na kasar Sin,kafin amariya ta shiga kofar gidan ango,dole ne ta ketare wata tasa wadda aka sa wuta a ciki,ma`anar wannan ita ce ana so a kuna dukkan abubuwa marasa sa`a,daga baya,zaman rayuwar sabon gidansu a nan gaba zai yi kyau kwarai da gaske.
Da farko dai,dole ne amariya da ango sun sunkuya sau uku,sau na farko,sun sunkuya ga sararin sama da kasa,sau na biyu,sun sunkuya ga iyayensu,sau na uku,sun sunkuya ga junansu.Daga baya,amariya da ango sun sha giya tare.
A gun bikin daura aure,dole ne a kira liyafa,abokai da dangogi na iyalin ango da na amariya su ci abinci su sha giya tare suna jin dadi domin taya murnar auren.Yayin da baki suke cin abinci,dole ne amariya da ango su ci abinci su sha giya tare da su saboda suna so su nuna godiya ga zuwan bakin.
Bayan liyafa,wato bayan da ango da amariya suka shiga dakin kwanansu,akwai wasa mai ban sha`awa,samari wadanda ba su daura aure ba sun fi so su yi irin wannan wasa,alal misali,ango da amariya sun yi sumba da juna a gaban dukkan baki ;ango ya saba amariya a kan bayansa,ya tafi tare da ita a gaban baki har ya gaji.Dukkan mutanen dake halartar bikin daura aure suna jin dadi.
Jama`a masu sauraro,kun dai saurari wani bayani game da al`adar daura aure ta kasar Sin.Wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na `Me ka sani game da kasar Sin` daga nan sashen Hausa na Redion kasar Sin.Mun gode muku saboda saurarenku.Da haka,Jamila take cewa,ku zaman lafiya.
|