Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-07 20:58:57    
Musulmin kasar Sin na murnar bikin bazara

cri

Bikin bazara, wani bikin gargajiya ne da ya fi jawo hankulan jama'ar kasar Sin, nan da shekaru fiye da dubu da suka wuce, Sinawa su kan yi shagulgulan iri daban daban masu ban sha'awa don nuna muranar bikin bazara. Yanzu, bikin bazara na shekarar 2008 yana kusantowa, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda musulmin kasar Sin ke taya murnar bikin bazara.

Masu sauraro, gasar wasannin Olympic na shekarar 2008 na birnin Beijing, wani babban labari ne da dukkan Sinawa ke zura ido a kai, tare da karantowar gaggaruwar gasar, bikin bazarar gargajiya na bana shi ma zai shiga wani irin halin annashuwar wasannin Olympic.

Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyara ga wani iyalin kabilar Hui da ke birnin Beijing. A lokacin da ake ambatar bambancin da ke tsakanin bikin bazara na shekarar 2008 da na da, mai gida malam Ma ya ce, "Abin da ya sa na fi nuna farin ciki a kai shi ne, a bana dukkan iyalinmu za mu yi murnar bikin bazarar gargajiya a wannan babban sabon gida. Bayan haka kuma, za mu gayyaci dangi da abokanmu zuwa gidanmu a lokacin bikin, kuma mu ci abinci tare."

Malam Ma ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yanzu muna iya zama a irin wannan sabon gida, lallai ya kamata mun yi godiya ga manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Bayan da aka soma gudanar da manufar, sai na fid da aiki mai dorewa, kuma na aiwatar da aikin ciniki da kana. Ta kokarin da na yi har shekaru da dama, yanzu na sayi babban gida, da kuma mota."

Ko da ya ke malam Ma yana da shekaru fiye da hamsin da haihuwa, amma yana son motsa jiki sosai. A zaman yau da kullum, ya kan kalli shirye-shiryen telibijin game da motsa jiki. Musamman ma bayan da birnin Beijing ya samu nasara wajen samun damar shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, malam Ma ya fi mayar da hankali kan bunkasuwar sha'anin motsa jiki na kasar Sin. Kan gasar wasannin Olympic da za a shirya a watan Oktoba na shekarar 2008 a nan birnin Beijing, malam Ma ya ce, "A shekarar 2004, kasarmu ta samu damar shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, a matsayina na wani Basine, na yi girman kai sosai kan wannan. Saboda wannan na nuna cewa, cikakken karfin kasarmu ya karu, har ma muna iya shirya gasar wasanni bisa matsayin duniya. Kazalika kuma wannan na nuna cewa, matsayin kasar Sin yana ta karuwa a duniya."

Bayan haka kuma, malam Ma ya gayawa wakilinmu cewa, ya shirya wani shirin musamman a lokacin bikin bazara na bana.

"A yau da kullum, mutane suna shan aiki sosai, musamman ma matasa ba su da isasshen lokaci don motsa jiki. Amma, yanzu lokacin hutu yana kusantowa, saboda haka, na odar filin wasanni, ta yadda dangogi da abokanmu za su iya buga kwallon tebur, da kwallon gashi."

Malam Ma ya ce, yanzu an riga an gama ayyukan gidajen wasanni da filayen wasanni guda 36 na gasar wasannin Olympic. A watan Yuni na shekarar da muke ciki kuma, layin jiragen karkashin kasa musamman na wasannin Olympic zai soma aiki. An yi imani cewa, kasar Sin za ta shirya wata gasar wasannin Olympic da ta fi kyau a tarihi. Muna maraba da masu wasannin motsa jiki, da abokanmu, da kuma 'yan uwanmu na musulmi daga kasashe daban daban na duniya.

A lokacin da muke kawo karshen ziyarar, malam Ma ya bayyana cewa, "Ina fatan ahleri ga Beijing."

Masu sauraro, bisa saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin, da kuma kara karuwar matsayin zaman rayuwar jama'ar kasar, hanyoyin murnar bikin bazara na jama'ar da ke wurare daban daban suna ta canjawa. Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyara ta hanyar buga waya ga Mu Xiaoli, wata daliba ta kabilar Hui, inda ta yi mana bayani kan yadda 'yan kabilar Hui ke taya murnar wannan bikin gargajiyar kasar Sin.

"Ni wata daliba ce daga jami'ar al'umma ta arewa maso yamma ta birnin Lanzhou na jihar Gansu, ni kuma wata musulmi. A ganina, bikin bazara ya sanya dukkan kasar Sin cikin halin farin ciki. Mu musulmi mu ma muna jin farin ciki sosai, kuma muna murnar bikin bazara tare da 'yan uwanmu na kabilar Han. A ranar 30 ga watan Disamba na kalandar wata, wato kalandar gargajiya ta kasar Sin, mu kan taru tare da dukkan iyalinmu, don cin abinci, da kuma kallon shirin murnar bikin bazara ta talibijin."

Kan canje-canjen da aka yi a 'yan shekarun da suka wuce, Mu Xiaoli ta ce, saboda iyalinta na fama da talauci a lokacin yarantakarta, don haka, ba su da isasshen kudi don murnar wannan bikin bazarar da ba na kabilarsu ba. Amma, tun bayan da aka aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, matsayin zaman rayuwarsu ya karu sosai. Mamar Mu Xiaoli ta gaya wa wakilinmu cewa, "A da iyalinmu na fama da talauci, har ma ba mu da isasshen kudi don sayen abinci masu dadin ci, da kuma kyakkyawan tufaffi. Amma, yanzu zaman rayuwarmu ya samu kyautattuwa sosai. Ba zan mai da hankali kan shirya kayayyaki don murnar bikin bazara ba, saboda na iya samun dukkansu a kantuna."

A da, yankin arewa maso yammacin kasar Sin ya ja da baya wajen bunkasuwar tattalin arziki da kuma al'adu. Amma, tare da ake aiwatar da manufar raya yankin yamma, matsayin tattalin arziki na yankin ya karu sosai, a waje daya kuma, an samun bunkasuwa sosai a fannonin al'adu, da motsa jiki, da dai sauransu. Yanzu, lokacin shirya wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing yana kara karantowa, jama'ar yankin arewa maso yamma suna cikin halin farin ciki na maraba da gasar wasannin Olympic. Mu Xiaoli ta ce, "Shirya gasar wasannin Olympic, wani gaggarumin lamari ne na kasarmu. A lokacin, jama'ar kasashe daban daban na duniya za su zo kasar Sin, kuma za su zo birninmu. Yanzu, ina kokari wajen koyon yaren Turanci, don gabatar da kasarmu, da garinmu ga abokaina kasashen ketare."