Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-07 20:48:05    
Cheng Fei, shahararriyar 'yar wasan lankwashe jiki ta kasar Sin

cri

Masu sauraro, barkanku da war haka, ni ce Tasallah, yanzu lokaci ya yi da muka fara shirinmu na wasannin motsa jiki. A cikin shirinmu na yau, da farko dai, bari in gabatar muku da wata shahararriyar 'yar wasan kasar Sin, wadda ta gwanance wajen wasan lankwashe jiki. Daga bisani kuma, sai wasu labaru game da wasannin motsa jiki.

A cikin gasar wasan lankwashe jiki bisa gayyata ta kasa da kasa ta 'Fatan alheri a Beijing' da aka yi a shekarar bara, 'yar wasa Cheng Fei, wato kyaftin din kungiyar wasan lankwashe jiki ta mata ta kasar Sin ta kwashe lambobin zinariya 3 a cikin shirin wasan tsallen kundunbala bisa sanda da na wasan motsa jiki a kan dabe da kuma na wasan taka-ka-fadi, ta nuna babban fifikonta sosai. A matsayinta na jagora ta kungiyar wasan lankwashe jiki ta mata ta kasar Sin, Cheng Fei ta fi fuskantar babban nauyi a cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara. Ko da yake tana kuruciya, amma wannan budurwa ta yi fintikau wajen jagorantar abokan kungiyarta domin samun nasara.

Cheng Fei ta zo daga birnin Huangshi na lardin Hubei da ke yankin tsakiya ta kasar Sin. Wannan kyakkyawar budurwamai yawan murmushi ba ta sha bambam da sauran 'yan mata sosai ba. Amma in kun waiwayi nasarorin da wannan budurwa mai shekaru 19 da haihuwa ta taba samu, to, za ku ji girgiza kwarai. Ta taba zama zakaru a gun wasu muhimman gasannin kasa da kasa.

A kasarmu, Cheng Fei ta shahara bisa tsallen kundunbala na Cheng Fei a cikin wasan tsallen kundunbala bisa sanda na mata. A cikin gasar fid da gwani ta wasan lankwashe jiki ta duniya da aka yi a shekarar 2005, a cikin shirin wasan tsallen kundunbala bisa sanda, Cheng Fei ta sami nasarar kammala wannan tsallen kundunbala mai matukar wuya. Hadaddiyar kungiyar wasan lankwashe jiki ta kasa da kasa ta nada wannan tsallen kundunbala mai wuya kwarai da sunanta, saboda kafin wannan, babu wadda ta iya kammala shi. Wannan shi ne karo na farko da sunan wata 'yar wasan kasar Sin ta bullo a cikin wasan tsallen kundunbala bisa sanda a tarihin wasan lankwashe jiki.

Cheng Fei ta koyi fasahar 'yan wasan lankwashe jiki ta maza wajen zayyana tsallen kundunbala na Cheng Fei, shi ya sa tsallen kundunbala din na da wuyar kammalawa sosai, ta haka mutane sun kalli Cheng Fei a matsayin ba yadda suka san ta a da. Amma duk da haka, wasan lankwashe jiki bai mammaye dukkan zaman Cheng Fei ba. Kamar yadda sauran 'yan mata suke yi, a lokacin hutu, Cheng Fei ta kan yi harkoki iri daban daban, ta gaya mana cewa, 'Na fi kishin kallon gasannin wasan kwallon kafa, kuma ina fi goyon baya kungiyar wasan kwallon kafa ta Arsenal ta kasar Birtaniya. Saboda ta kan kai wa abokan takararta hari da kyau. A galibi dai, tana da kyau kwarai.'

Wata budurwa tana kishin kallon gasannin wasan kwallon kafa? Lalle Cheng Fei ta yi kama da namiji a wasu fannoni. A idon malam Liu Qunlin, malamin horas da wasanni da ke horar da Cheng Fei, Cheng Fei mai kishin wasan kwallon kafa ce mai suna a kungiyar kasar Sin, amma a sa'i daya kuma, tana son karanta littattafai ainun. Ya gaya mana cewa. 'Ta fi son karanta littattafan gargajiya da kuma littattafai dangane da tarihin kasar Sin. Tana son karanta littattafai game da yadda ake yin amfani da kwakwalwa.'

Littattafan tarihi sun kyautata halayen Cheng Fei, sun kuma sanya ta kan kwantar da hankalinta. A ganin malam Liu, Cheng Fei tana son karatu, tana kuma da tunani. A cikin gasa, ta kan mai da hankalinta a dukkan fannoni, ta kuma nuna gwanintarta yadda ya kamata. Ya ce, 'A lokacin gasa, ta kan yi la'akari da dukkan fannoni domin warware matsala. Ko da yake tana kuruciya, amma ta iya share fagen gasanni yadda ya kamata, ta fito da tsarinta kan share fagen gasanni.'

Kamar yadda malam Liu ya fada, Cheng Fei ta kan daidaita dukkan abubuwa a tsanake. Ta kan sha yin tunani domin koyon sabon motsi, har zuwa ta iya yinsu da kyau. Ko a zamanta ko a lokacin horaswa ko a cikin gasanni, Cheng Fei ta kan gamu da matsaloli da yawa, ammata ce, 'Ina fatan in kara nuna jaruntaka a lokacin da nake fuskantar matsaloli, haka kuma in gaya mini cewa, wajibi ne in nuna aniyar warware su.'

A yayin da aka kaddamar da aikin horaswa na lokacin dari a watan Nuwamba na shekarar bara, an nada Cheng Fei a matsayin kyaftin kungiyar kasar Sin, tana jagorantar kungiyar kasar Sin yadda ya kamata. Malam Liu ya yi farin ciki bisa ayyukan da Cheng Fei ta yi, ya ce, 'Wannan budurwa ta kan nuna halin karimci. Ta zama tare da saura yadda ya kamata. A takaice dai, a lokacin da Cheng Fei take jagorantar kungiyar kasar Sin, ana tabbatar da kwanciyar hankali a kungiyar, kungiyarmu na cikin hali mai kyau.'

A cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara, Cheng Fei da abokan kungiyarta za su yi namijin kokari domin samun lambar zinariya, ta bayyana cewa, samun lambar zinariya a mahaifarta kasar Sin burinta ne, tabbas ne za ta darajanta wannan kyakkyawar dama.