Bikin bazara bikin gargajiya mafi muhimmanci ne a nan kasar Sin. Amma a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, wasu yankunan kudancin kasar Sin sun gamu da bala'in ruwan sama da dusar kankara da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Sabo da haka, lokacin da jama'ar dukkan kasar Sin suke maraba da bikin bazara, shugabannin kasar Sin sun sake komawa yankuna masu fama da bala'in domin nuna jaje da gaisuwa ga jama'a masu fama da bala'in.
A ran 5 ga wata da yamma, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar ya je birnin Guilin musamman domin rangadin aikin fama da bala'in da ake yi a birnin. A filin jirgin sama, shugaba Hu Jintao ya yi jigilar kayayyakin jin kai tare da sojoji wadanda suke ajiye kayayyaki cikin jirgin sama. A ran 6 ga wata da safe, Hu Jintao ya isa gundumar Ziyuan inda ake fama da bala'in mafi tsanani. A kan hanyar tudu mai kwana da yawa, Hu Jintao ya nuna jaje ga 'yan kwadago wadanda suke gyara tsarin jigilar wutar lantaki cewa, "Yau, jajibirin bikin bazara ne, amma har yanzu kuna fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara kuna kokarin gyara tsarin jigilar wutar lantarki domin tabbatar da samar da wutar lantarki. Muna fatan za ku iya kawar da dukkan matsaloli domin samar da wutar lantarki ga gidajen farar hula tun da wuri. Na sake nuna muku godiya cikin sahihanci."
Tun daga tsakiyar watan Janairu na shekarar da muke ciki, kamar sauran yankunan kudancin kasar Sin, birnin Guilin, da ya yi suna sosai a duk duniya wajen yawon shakatawa a nan kasar Sin, ya gamu da bala'in, inda mutane miliyan 2 da dubu 680 suka shiga cikin mawuyacin hali.
Yan Defa, wani manomi ne na gundumar Ziyuan da ke cikin tsaunuka. Suna neman kudi ta hanyar shuka bamboo. Mr. Hu ya gaya masa cewa, "Ko da yake muna birnin Beijing, amma muna begenku, sabo da haka, na zo nan yau musamman domin nuna muku gaisuwa. "
A cikin gidan Yan Defa, Mr. Hu ya zauna tare da sauran manoma ya tambaye su kan yadda suke fama da bala'in. Bayan da ya samu labari, cewa sun riga sun samu tallafin kudi daga gwamnatin wurin, ya ce, "Yanzu, nauyin da ke bisa wuyanmu mafi muhimmanci yanzu shi ne kulawa da zaman rayuwar farar hula, musamman farar hula wadanda suke fama da talauci. Dole ne a tabbatar da samar musu abinci da tufafi da bargunan maganin sanyi, kuma za su iya samun jiyya idan sun kamu da ciwo. Sannan kuma, bayan bikin bazara, dole a yi kokarin kawo albarka da sake raya garinmu."
A kan hanyar tudu, wasu motoci masu daukar kayayyakin jin kai sun sadu da motocin Hu Jintao. Hu Jintao ya sauka daga mota ya gaya wa hafsoshi da sojoji cewa, "Yau jajibirin bikin bazara, gobe rana ce ta bazara. Dole ne mu isa da dukkan kayayyakin jin kai da jama'a suke bukata cikin gaggawa sabo da za su iya murnar bikin bazara lami lafiya."
Bugu da kari kuma, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya je lardin Guizhou domin ba da jagoranci ga aikin fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara. A kauyen Guanyin da tsayinsa ya kai mita 1200 daga leburin teku, Wen Jiabao ya bi wata karamar hanyar tudu ya taka kankara mai laushi ya isa kolin tudun Guanyin domin gai da 'yan kwadago wadanda suke gyara tsarin jigilar wutar lantarki. "Kuna kokari. Na zo nan na gaishe ku, na taya ku murnar bikin bazara. Lokacin da ake murnar bikin bazara, kuna ci gaba da yin aikinku a gurabanku na gyara tsarin jigilar wutar lantarki. Na gode muku da iyalanku kwarai da gaske."
|