Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-07 17:18:06    
Mutane na wurare daban daban a kasar Sin sun yi murnar bikin bazara

cri

Ran 7 ga wata, bikin bazara ne bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Mazauna wurare daban daban na kasar Sin sun yi murnar bikin bazara ta hanyoyi daban daban.

A matsayinsa na birnin da zai sami bakuncin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, birnin Beijing ya kira bukukuwan wasannin nishadi na gargajiya na kasar Sin iri daban daban fiye da 20. Matasa kuwa sun taya wa juna murnar bikin bazara ta hanyoyin aika da gajerun labaru ta wayar salula da kuma wasiku a kan yanar gizo ta Internet. Amma wadannan harkoki sun sha bamban da wadanda aka yi a shekarun baya, suna da nasaba da wasannin Olympic a shekarar da muke ciki.

A kwanaki 20 da suka wuce, yawancin wurare a kudancin kasar Sin sun gamu da bala'un ruwan sama da dusar kankara. A sakamakon ayyukan yaki da bala'un da kuma kyautatuwar yanayi, an maido da aikin sufuri da zirga-zirga da kuma samar da wutar lantarki a wadannan wurare. Kasar Sin ta riga ta dauki matakai da dama domin tabbatar da kai isassun kayayyaki a kasuwa. Sa'an nan kuma, an yi wasan wuta da bukukuwan wasannin nishadi na gargajiya na kasar Sin da sauran harkokin gargajiya a wadannan wurare.

Kazalika kuma, a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur da jihar Tibet masu ci gashin kansu, mazauna 'yan kabilu daban daban sun yi murnar bikin bazara tare.(Tasallah)