Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-07 16:58:53    
Tauraron dan Adam kirar Chang'e ya taya Sinawa murnar bikin bazara na gargajiya daga duniyar wata

cri

Ran 6 ga wata, wato a jajibirin bikin bazara bisa kalandar kasar Sin, tauraron dan Adam kirar Chang'e mai lamba 1 da kasar Sin ta harba a karo na farko domin yin binciken duniyar wata ya aiko da muryar musamman daga duniyar wata mai nisa domin taya Sinawa murnar bikin bazara.

Abubuwan da aka tanada cikin wannan murya da aka aiko da ita daga wurin da ke nisan kilomita dubu 38 a tsakaninsa da duniyarmu su ne, tauraron dan Adam kirar Chang'e mai lamba 1 ya taya kowa da kowa murnar bikin bazara daga duniyar wata. Ya kuma aika da wani kide mai suna 'kide-kiden murnar bikin bazara' daga duniyar wata.

Ban da wannan kuma, a ran 6 ga wata, a birnin Lausanne na kasar Switzerland, Hein Verbruggen, wani jami'in kwamitin wasan Olympic ta kasa da kasa kuma shugaban kwamitin kula da harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ya taya Sinawa murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ya kuma nuna fatan alheri da cewa, za a sami nasarar kiran gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing.

Kazalika kuma, a jajibirin bikin bazara na gargajiya na kasar Sin, shugaba Bush na kasar Amurka ya taya wadanda ke zama a Amurka da kuma duk duniya, amma asalinsu 'yan kasashen Asiya murnar sabuwar shekara, wato shekarar bera.(Tasallah)