Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-06 21:11:05    
Wasu kide-kiden taya murnar bikin bazara na kasar Sin

cri

Yau ranar karshe ta wata na 12 na shekarar 2007 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Gobe ranar farko ce ta sabuwar shekara bisa kalandarmu. Sabo da haka, lokacin da muke kama sabuwar shekara, bisa al'adar al'ummomin kasar Sin, da farko dai bari mu ce muku "barka da sabuwar shekara". Muna fatan dukkanku za su sami koshin lafiya da arziki a cikin sabuwar shekara.

Jama' a masu saurarao, wannan kida mai suna "muna farin ciki sosai" da kuka saurara yana bayyana yadda al'ummomin kasar Sin suke murnar wannan bikin bazara, wato biki mafi muhimmanci a nan kasar Sin, kamar babbar sallah a kasashe masu bin addinin Musulunci. Yanzu ga wani kida daban da ke bayyana yadda fararen hula Sinawa suke murna lokacin da suke barka da sabuwar shekara.Jama'a masu sauraro, kidan da kuka saurara shi ne "barka da lokacin bazara da fatan alheri". Bisa al'adar kasar Sin, lokacin da ake bikin bazara, a kan manna kalma "alheri" a kan kofa da bango domin bayyana yadda Sinawa suke neman fatan alheri. To, yanzu ga wani kida daban mai suna "neman fatan alheri". 

To, jama'a masu sauraro, kidan da kuka saurara shi ne "neman fatan alheri" da yake barkuwa a nan kasar Sin. Lokacin da ake kai ziyarar ban girma ga abokai da iyalai, Sinawa su kan fadi cewa, "ina fatan za ka samu arziki cikin sabuwar shekara." Yanzu za mu gabatar muku wani kida mai suna "Allah ya ba ka arziki".

To, madalla, jama'a masu sauraro, kidan da kuka saurara shi ne "Allah ya ba ka arziki". Yanzu dai ga wani kida daban mai suna "Kwanakin da ke cike da farin ciki". Wannan kida yana karbuwa a yankunan arewacin kasar Sin. A cikin wannan kida, ana bayyana yadda ake farin ciki sosai lokacin da ake murnar bikin bazara.

Jama'a masu saurare, kidan da kuka saurara shi ne "kwanakin da ke cike da farin ciki" da yake karbuwa a yankunan arewacin kasar Sin. Yanzu ga wani kida daban da ake rerawa a nan kasar Sin domin murnar bikin bazara, wato biki mafi muhimmanci a nan kasar Sin a gare fararen hula Sinawa. Wannan kida shi ne "murnar sabuwar shekara".

Bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ran 7 ga wata na Fabrairu na shekarar da muke ciki, ranar farko ce ta wata sabuwar shekara. Bisa al'adar kasar Sin, a wannan rana, dukkan iyalai suna murnar sabuwar shekara tare. Sabo da haka, yanzu ga wani kida daban mai suna "iyalai suna murnar sabuwar shekara tare".

Jama'a masu sauraro, lokacin da ake murnar sabuwar shekara a nan kasar Sin, kanana su kan kai ziyarar ban girma ga manya. A waje daya kuma, abokai da iyalai suna kai wa juna ziyarar ban girma domin isar da dimbin gaisuwa da fatan alheri. Yanzu ga wani kida daban mai suna "kai ziyarar ban girma domin murnar sabuwar shekara".

Jama'a masu sauraro, ba ma kawai ana kai ziyarar ban girma ba, har ma ana shirya shagulgula iri daban-dabam lokacin da ake murnar sabuwar shekara a nan kasar Sin. Yanzu ga wani kida mai suna "muna murnar sabuwar shekara tare".

To, jama'a masu saurare, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na kide-kiden al'ummomin kasar Sin. Muna fatan masu saurarenmu za su iya samun fatan alheri da arziki a ciki sabuwar shekara. Sanusi ya shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya. (Sanusi Chen)