Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-06 21:06:45    
Yau jajibiri ne na sallar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin

cri

I: Barkanmu da saduwa da ku a cikin shirin musamman da muka tsara don bikin bazara na kasar Sin.

S: Alhaji Ilelah, ko ka sani? Yau wata rana ce ta matukar musamman ga dukkan Sinawa na duk duniya.

I: Ko shakka babu, na sani. Yau jajibiri ne na sallar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Kuma Sinawa su kan kira sallar da suna"bikin bazara". Masu sauraro, bikin bazara biki ne mafi muhimmanci a cikin wata shekara ga dukkan Sinawa, ko suna da zama a babban yankin kasar Sin, ko suna shiyyar HongKong da ta Taiwan da ta Macao ta kasar Sin, har ma ko suna zama a sauran kasashe da yankuna na duniya. Amma mene ne dalilin da ya sa ba a yin sallar sabuwar shekara ta kasar Sin a ran 1 ga watan Janairu ba?

S: Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kasar Sin tana da kalandarta wadda aka tsara ta bisa yanayin aikin gona. Kuma an yi bikin bazara ne don taya murnar zuwa sabuwar shekara, shi ya sa a kan yi bikin a ran 1 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Amma wannan lokaci ya kan sha bamban lokacin da ake nuna shi bisa kalandar da ake yin amfani da ita a duk duniya. Kullum a kan yi bikin bazara daga karshen watan Janairu zuwa tsakiyar watan Fabrairu. Bisa labarin da aka samu daga littattafan tarihi, an ce, bikin baraza wato sallar sabuwar shekara ta kasar Sin tana da dadadde har na tsawon fiye da shekaru dubu hudu.

I: Lalle bikin bazara yana da dogon tarihi. Tare da sauyin zamani da kuma bunkasuwar zaman al'umma, yawan ire-iren harkokin da Sinawa su kan yi don taya murnar bikin bazara ya samu karuwa sosai. To yanzu za mu gabatar muku da yadda Sinawa su kan yi bikin bazara.

I: A ganina, idan an tabo bikin bazara, to dole ne masu sauraronmu za su yi tambayar, cewa mene ne dalilin da ya sa Sinawa su kan kira sallar sabuwar shekara da suna "bikin bazara"?

B: Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kasar Sin wata kasa ce wajen aikin gona tun zamanin da, kuma wannan yana da nasaba da matsayinta a taswira da yanayinta. Kasar Sin tana arewacin bangaren duniya, kuma an kasa fasaloli hudu a wata shekara, wato lokacin bazara da lokacin zafi da lokacin kaka da kuma lokacin hunturu. Sabo da ana yin matukar sanyi da kuma dusar kankara a lokacin hunturu, shi ya sa tun tuni a kan jira zuwan lokacin bazara inda ake iya samun yanayi mai dumi da kuma furanni masu kyan gani. Haka kuma game da wata al'umma ta aikin gona, kaddamar da aikin shuke ire-ire a lokacin bazara wata alama ce ta zuwan wata sabuwar shekara. In an fara yin bikin bazara, sai a alamta cewa, lokacin bazara yana zuwa, bishiyoyi da ciyayi za su farfado, kuma za a kaddamar da aikin shuka ire-ire, daga baya kuma za a samu girbi.

I: To, yanzu bari mu shakata kadan, da wani kida na gargajiyar kasar Sin wanda ake kiransa "maraba da zuwan lokacin bazara cike da murna".

I: A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata da nake da zama a kasar Sin, na gano cewa, ko da yake yawan lokacin hutu don bikin bazara yana da kwanaki 7 kawai bisa doka, amma a hakika dai Sinawa su kan fara share fage daga kwanaki fiye da 20 kafin zuwan bikin bazara. Na farko shi ne, ko wane gida ya kan yi shara da kuma sayen abinci da kayayyaki don sallar sabuwar shekara.

S: E, madalla. Sinawa su kan kira kwanaki daga ran 23 zuwa ran 30 ga watan Disamba na ko wace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin "ranar maraba da lokacin bazara", ko kuma "ranar tsabta dakuna". Wato an tsabta dakunan kwana kwata kwata kafin bikin bazara domin kau da talauci da kuma abubuwa masara sa'a, daga baya kuma an yi wa dakunan ado. Alal misali, kafin bikin bazara, Sinawa su kan manna wata takarda mai launin ja a ko wane gefen babbar kofa ta dakunan kwana, wadda a kan rubuta fatan alheri na sabuwar shekara a kanta, kuma a kan kira wadannan takardu biyu "Chunlian". Ban da wannan kuma a kan rataya fitilu masu launin ja a gaban babbar kofa, da kuma manna takardar da aka rubuta kalmar "fatan alheri" a kai da kuma zane-zanen gunkin kudi da kuma gunkin bakin kofa a kan babbar kofa. Haka kuma a kan manna zane-zane masu launi iri daban daban da suke da ma'anar fatan alheri a cikin gida, budurwoyi kuwa su kan yanka takardu masu launin ja zuwa sifar furanni, daga baya kuma aka manna su a kan tagogi. An yi dukkan wadannan 'yan mata ne domin maraba da sabuwar shekara cikin tsabtattacen muhali da kuma murna. Haka zalika kuma wani mihimmin aiki daban shi ne sayen kayayyakin bikin bazara.

I: kayayyakin bikin bazara su ne abincin da za a ci da kuma kayayyakin da za a yi amfani da su a lokacin bikin bazara, ko ba haka ba? Kuma su kan hada da abinci iri iri da za a ci a lokacin hutu na bikin bazara, da halawa da 'ya'yan itatuwa da kuma kalaci da za a bai wa 'yan iyali da kuma abokai lokacin da suke kawo ziyara, da sabbin tufafi da kayayyakin wasan yara da za a bai wa yara, da kuma kyautar da za a bai wa sauran 'yan iyali.

S: E, haka ne. sabo da haka game da Sinawa da har kullum su kan yi kwazo da kuma tsimin kudade, suna iya kashe kudade mafi yawa a lokacin biki bazara.

I: Wasu abokaina Sinawa sun gaya mini cewa, yanzu zaman rayuwarsu ya samu kyautatuwa, shi ya sa suke yi kamar a yi ta yin bikin sallar sabuwar shekara a ko wace rana. A lokacin da, a kan jira bikin bazara sosai, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da muddin a bikin bazara, sai a iya kashe kudade wajen sayen abinci mai dadi da kuma canja tsoffin tufafi. Amma a zamanin yau, ana iya sayen abinci da yake so a ko wane lokaci, kuma sayen sabbin tufafi ba zai kashe yawan kudade ba, shi ya sa ba za a bukaci jiran bikin bazara wajen sayen wadannan kayayyaki ba. Ta haka, yanzu ba a yi Allah Allah wajen jiran bikin kamar yadda aka taba yin a lokacin da.

S: E, gaskiya ne. Amma a ganina, in an ce, yanzu ba a yi Allah Allah wajen jiran bikin bazara kamar lokacin da ba, to ya fi kyau a fadi cewa, abubuwan da ake jira a bikin bazara sun sha bamban. Kamar ni, yanzu dalilin da ya sa nake jiran bikin bazara shi ne sabo da zan iya hutawa a wannan lokacin hutu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne bikin bazara wani biki ne wajen haduwa da 'yan iyali tare. Kome nisa, ko wane Basine zai yi iyakacin kokarinsa wajen koma garinsa a lokacin bikin bazara. Sabo da haka, koma gida wani muhimmin take ne na bikin bazara har abada, wanda ba a canja shi ba a cikin wadannan dimbin shekarun da suka gabata.

I: A duk lokacin da ake taya murnar bikin barana, dukkan Sinawa da suke aiki ko kuma karatu a wurare daban daban na kasar su kan bi wannan al'adar gargajiya da suka saba bi, wato komawa gari domin sake saduwa da iyalansu, shi ya sa kwaram yawan fasinjoji ya karu sosai a duk kasar. A shekarar da muke ciki, da idona na ga yadda Sinawa suke neman komawa gida domin sake saduwa da iyalansu kafin bikin bazara. A ko wace tashar jiragen kasa da filin jiragen sama da tashar motoci masu dogon zango, an sami cunkuson mutane, wadanda suke jiran komawa gida da kuma wadanda suka sauka ba da dadewa ba. Sa'an nan kuma, a wani muhimmiyar tashar jiragen kasa a Beijing, hedkwatar kasar Sin, an bude tagogin sayar da tikiti guda 130. A gaban ko wace tagar kuwa, layin mutanen da suka neman sayen tikiti ya kai tsawon mita dari 1 ko fiye. A kasar Sin, yawancin mutane su kan zabi shiga jiragen kasa in suna bukatar zuwa wani wuri mai nisa. Ma'aikatar kula da harkokin hanyar dogo ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, a wannan shekara, a cikin kwanaki 40 kafin bikin bazara da kuma wasu 40 bayan bikin bazara, mutane kimanin miliyan 180 sun shiga jiragen kasa domin kaiwo da kawowa. Ko a kasar Sin mai yawan mutane bililyan 1 da miliyan 300, wannan adadi wato miliyan 180 ya girgiza mutane kwarai.

S: A, wannan gaskiya ne. Kwanaki 40 kwanaki 40 kafin bikin bazara da kuma wasu 40 bayan bikin bazara lokaci ne da dukkan mutanen Sin suka fita waje domin yin ziyara, har ma dimbin Sinawa da suke karatu ko kuma yin aiki a ketare sun yi hanzari da komawa kasar Sin kafin bikin bazara domin sake saduwa da iyalansu. Sa'an nan kuma, wadanda ba su iya komawa garinsu su kan buga wayar tarho ko kuma aiko da wasika zuwa iyalansu daga wurare masu nisa domin gaya wa iyalansu cewa, kome ya yi kyau a gare shi. Suna kuma nuna musu fatan alheri domin bikin bazara.

I: Bisa labarun da aka bayar, na ji an ce, gwamnatin Sin ta fi mayar da mutane a gaba da kome wajen tsara lokacin hutu na bikin bazara a shekarar da muke ciki. Ko ba haka ba?

S: Eh, haka ne. gwamnatinmu ta yi gyare-gyare kan lokacin hutu. Za mu fara hutunmu daga jajibirin bikin bazara a maimakon daga rana ta farko ta sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, ta haka 'yan kwadago suna iya komawa gida, su ci abinci tare da iyalansu a jajibirin bikin bazara.

I: Ga alama cewa, tabbas ne za su ci abinci tare cikin murna a wannan shekara, in an kwatanta da na da.

S: A, madalla. Jajibirin bikin bazara, dare ne kafin sabuwar shekara, shi ne kuma daren da mambobin iyalai suka sake saduwa da juna. Abincin dare da a kan ci a wannan dare wata alama ce da ta nuna cewa, dukkan mambobin iyalai suna sake saduwa da juna. To, yanzu bari mu ji wata waka mai suna 'abinci na sake saduwa da iyali'.

(??4,????????)

S: A jajibirin bikin bazara, wato a lokacin da muka yi ban kwana da tsohuwar shekara, kuma mun zura ido kan sabuwar shekara, bayan da suka ci abinci na sake saduwa da iyali, dukkan iyali sun taru sun zama, ba su yi barci har duk dare ba domin maraba da sabuwar shekara. Abun da Sinawa su kan yi na matsayin daya daga cikin harkokin gargajiya mafi muhimmanci da su kan yi domin murnar sabuwar sheakra.

I: I, na san wannan. Wannan lokaci lokaci ne da yara suka fi yin farin ciki. Manya suna taruwa, su zauna tare da cin busasshun 'ya'yan itatuwa da danyun 'ya'yan itatuwa, sunn yin hira tare, suna kallon telibijin, suna yin wasan dara da wasan karta. Yara kuwa, sun fi son wasan wuta.

(??5,???,?????)

S: Misalin karfe 12 da daddare a jajibirin bikin bazara, wato daidai lokacin da ake yin ban kwana da tsohuwar shekara, ana yin maraba da sabuwar shekara, amon wasan wuta da dariya da amon kwararrawar maraba da sabuwar shekara da kuma fatan alheri da mutane suna nuna wa juna sun hadu da juna. A cikin ko wane gida, ana iya ganin cewa, kowa da kowa yana farin ciki sosai, ana shimfida kwanciyar hankali a ko wane gida. Irin wannan lokaci lokaci ne da yara su kan zura idonsu a kai, kuma shi ne lokacin da yara suka fi yin farin ciki. Sun taya wa masu shekaru murnar sabuwar shekara, masu shekaru kuwa nan da nan ne suka ba su kyautar kudin murnar sabuwar shekara.

I: Masu shekaru su kan ba na kasa da su wajen shekaru kyautar kudi, wannan shi ne al'adar gargajiya da Sinawa suke bi a lokacin murnar sabuwar shekara. Yawan irin wannan kudi ba ya da muhimmanci sosai, shi ne fatan alheri da aka nuna wa yara, ana fatan za su ji dadin zamansu. To, yanzu bari mu saurari wata waka mai suna 'amon kayan wasan wuta mai dadin ji'.

(??6,???????)

S: Masu sauraro, yau jajibirin bikin bazara ne. A daidai wannan lokaci, a ko ina a kasar Sin, birane da kuma yankunan karkara cike suke da farin ciki. Kowa da kowa na nitsuwa a cikin kyakkyawan yanayi, yana fatan zai ji dadin zamansa a sabuwar shekara.

I: Yauwa, madalla. Kashegari za mu shiga sabuwar shekara. Maza da mata, tsoffi da yara kowa da kowa su kan sanya kyawawan tufafi da kayan ado. Da farko su kan taya wa masu shekara murnar sabuwar shekara, daga gaba, dangogi da aminai su kan taya wa juna murnar sabuwar shekara. Yanzu ina so in taya wa abokaina na kasar Sin murnar sabuwar shekara. Ko ka iya koya mini yadda muka ce, barka da sabuwar shekara da Sinanci? Ina tsammani cewa, tabbas ne dimbin masu sauraronmu za su nuna sha'awa kan koyon wannan jimla.

S: I, mana. 'Xin Nian Hao!' Masu sauraro, ko ka tuna da wannan jimlar? A madadin dukkan ma'aikatan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin, mun taya muku murnar sabuwar shekara. Muna fatan a cikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, kome da kome zai yi kyau a gare ku.

I: Gobe rana ce ta farko ta sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Gobe da war haka, za mu ci gaba da shirinmu na musamman game da bikin bazara na gargajiya na kasar Sin, za mu yi muku bayani kan al'adun gargajiya da Sinawa suke bi a bikin bazara. Muna muku godiya da saurarenmu. Sai gobe da war haka, in Allah ya kai mu.