Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-06 20:54:54    
Shayar da nono zai iya ba da taimako wajen kiwon lafiyar mata da kuma jariransu

cri

Bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Afirka ta Kudu suka yi nazari, sun gano cewa, a cikin jariran da shekarunsu bai zarce watanni shida ba, game da wadanda suka sha nonon iyaye mata kawai, yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau daga iyayensu mata kadan ce sosai, idan an kwatanta su da wadanda suka sha garin madara.

Bisa wani bayanin da jaridar kasar Kenya ta bayar a ran 1 ga watan Afril na shekarar da muke ciki, an ce, masu ilmin kimiyya na cibiyar nazarin kiwon lafiya da yawan mutane ta Afirka sun bayyana cewa, game da jariran da shekarunsu ya kai daga makwanni shida zuwa watanni shida, idan sun sha nonon iyayensu mata kawai, to yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau daga iyayensu mata za ta kai kashi 4 cikin dari kawai, amma game da jariran da suka sha garin madara da kuma nonon dabbobi, yiyuwar kamuwa da cutar za ta ninka sau daya, wato za ta kai kashi 8 cikin dari, haka kuma idan jarirai suna cin sauran abinci ban da nono, to yiyuwar kamuwa da cutar za ta ninka kusan sau 10.

Masu ilmin kimiyya sun yi bayani cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da abinci ya kan kunshi sinadari mai gina jiki da yawa, wadanda suke iya lallata fatar da ke cikin cikin jarirai, ta haka kwayoyin cutar kanjamau za su fi saukin shiga ciki.

Ban da wannan kuma sun bayyana cewa, a kasashe masu ci gaba, sabo da ana yin amfani da dabarar yaki da sinadarin retrovirus wajen shawo kan cutar kanjamau, da samar da abinci ga jarirai kamar yadda ya kamata, da kuma ba da tabbacin jiyya, shi ya sa yawan jariran da ke kamuwa da kwayoyin cutar kanjamau daga iyayensu mata ya ragu daga kashi 25 zuwa kashi 2 cikin dari. Amma ba a yada wadannan dabaru a kasashe masu tasowa ba, shi ya sa masu ilmin kimiyya suna ganin cewa, ya fi kyau a kara yada dabarar samar da nonon iyaye mata a kasashe masu tasowa wajen shawo kan yaduwar cutar kanjamau.

Bisa labarin da mujallar 'Sabbin masu ilmin kimiyya' ta bayar, an ce, manazarta na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga nas-nas 96648 da suka haihu daga shekara ta 1986 zuwa shekara ta 2002. Daga baya kuma sun gano cewa, hadarin kamuwa da cutar zuciya ga matan da suka shayar da nono ga jariransu har shekaru biyu kadan ne sosai idan an kwantanta su da matan da ba su taba shayar da nono ga jarirai ba.

Manazarta sun bayyana cewa, watakila shayar da nono ga jarirai zai ba da taimako ga mata wajen canja sauye-sauyen halitta daga salon irin na samun ciki zuwa salon kamar yadda ya kamata. Lokacin da mata suke da ciki, a kan fi samun kitse mai yawa a cikin jikinsu, haka kuma yawan sinadarin fatty acid da ke cikin jininsu yana yin yawa a gwargwado. Ta hanyar shayar da nono ga jarirai, mata za su iya canja wadannan kitsen da ke jikinsu zuwa abubuwan gina jiki da jarirai suka bukata.

Mr. Alison da ya kula da wannan binciken ya ba da shawarar cewa, ya fi kyau mata sun shayar da nono ga jarirai har watanni 3 zuwa shekara guda bayan da suka haihu.