Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-06 19:19:02    
Sinawa suna maraba da bikin bazara ta hanyoyi daban daban

cri

Yau ran 6 ga wata, jajibiri ne na bikin bazara, wato biki ne mafi muhimmanci ga Sinawa, kuma rana ce ta karshe ta shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A wannan rana, mutane suna share fagen yin ban kwana da tsohuwar shekara, kuma maraba da sabuwar shekara. A shekarar bana, mutanen Sin sun fara lokacin hutu na murnar bikin bazara a jajibiri a maimakon rana ta farko ta sabuwar shekara, ta haka sun sami karin lokaci domin share fagen wannan muhimmin biki.

Bikin bazara yana da muhimmanci sosai ga Sinawa, kamar yadda Musulmai suke dora muhimmanci kan babbar salla. A gun bikin bazara na ko wace shekara, a ko ina a kasar Sin, mutane su kan yi alla-alla wajen maraba da sabuwar shekara. Ko da yake a shekarar bana, ana shan wahalar bala'un ruwan sama da dusar kankara a yawancin wuraren kudancin kasar Sin, wadanda ba a taba ganin irinsu a shekaru gomai da suka wuce ba, amma hakan bai raunana murnar Sinawa ba. Ko da yake wasu fasinjoji ba su iya komawa gida cikin lokaci ba a sakamakon ruwan sama da dusar kankara, amma hukumomin Sin da abin ya shafa da kananan hukumomin wurare sun bayyana cewa, sun yi namijin kokari wajen bai wa wadannan fasinjoji abinci da wurin kwana da wuraren nishadi da hutu, ta haka sun iya murnar bikin bazara.

Wang Wenxuan yana aiki a birnin Haikou a kudancin kasar Sin. A shekarun baya, ya kan yi hanzarin komawa gida da ke birnin Wanning daga Haikou domin cin abinci tare da iyalinsa a jajibirin bikin bazara bayan da ya gama aiki. Ya gaya mana cewa,'A da ban huta ba a jajibirin bikin bazara, shi ya sa iyayena su kan share fagen bikin bazara. Amma a shekarar bana, na sami dama, zan sayi kayan wasan wuta, zan yi murnar bikin bazara tare da iyalina.'

Kamar yadda Wang Wenxuan ya yi, in ba su da ayyukan musamman, yawancin mutanen Sin su kan koma gida a jajibirin bikin bazara da dare, su kan ci abinci na sake saduwa tare da iyalansu. Matasa su kan taya wa na gaba da su murnar sabuwar shekara, tsoffi ko dattijai kuma su kan bai wa na kasa da su kyautar kudi.

A idon mutane, an fi samun kyakkyawan yanayin murnar bikin bazara a arewa maso gabashin kasar Sin. A nan, baya ga ba da kyautar kudi, mazauna wuraren su kan bi dimbin al'adun gargajiya na kasar Sin. Madam Xing Lijuan da ta zo daga birnin Jilin na lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar Sin, ta gaya wa wakilinmu cewa, yau da wata guda da ta wuce, ta riga ta fara share fagen bikin bazara. Ta ce,'Mun manna kyawawan zane-zanen takarda da aka yanke da almakashi a kan bango da tagogi. Mun kayatar da dakuna da kyau. Sa'an nan kuma, mu kan rataye jajayen fitilu a ko wane gida. In an hango daga nesa, an shafa wa manyan gine-gine launin ja. A kan sami yanayin murnar bikin bazara sosai.'

Kamar yadda a kan ba da kyautar kudi, yin wasan wuta wata harka ce daban da a kan yi a gun bikin bazara. Xing ta gaya mana cewa, a arewa maso gabashin kasar Sin, tun daga karfe 10 da dare, a kan fara yin wasan wuta. Ta ce,'Dukkan sararin sama cike yake da kyawawan abubuwan wasan wuta masu launuka daban daban. Suna da kyan gani kwarai. In an hango ta taga, to, sai a iya ganin dusar kankara a waje. Yara suna wasa a kan dusar kankara, suna ihu, suna dariya. A kan yi wasan wuta har na tsawon awoyi 2 zuwa 3.'

A gaskiya, a wurare daban daban na kasar Sin, mutane kan yi murnar bikin bazara ta hanyoyi daban daban kuma bisa al'adun gargajiya daban daban. Amma a lokacin da sabuwar shekarar 2008 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin tana kan hanya, wadda take da ma'anar musamman ga Sinawa, dimbin mutanen Sin sun bayyana burinsu na bai daya, wato suna alla-alla wajen zuwa Beijing domin kallon gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 da kuma mara wa 'yan wasan kasar Sin baya domin samun karin lambobin zinariya.(Tasallah)