Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 20:11:19    
Bala'in dusar kankara ba zai yi illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba

cri

Bala'in ruwan sama da dusar kankara da ke faruwa a yankunan da ke kudancin kasar Sin a jerin 'yan kwanakin nan da suka gabata ya kawo wahala sosai ga aikin samarwa da zaman rayuwar jama'a na yankuna masu fama da bala'in, haka kuma ya yi illa ga tattalin arzikin wurin. Amma jami'ai da kwararru na kasar Sin a fannin tattalin arziki sun nuna cewa, ko da yake an samu hasara sakamakon bala'in, amma wannan ba zai yi illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba a nan gaba. To, yanzu ga cikakken bayani.

Tun ran 10 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, ana ta yin sanyi da ruwan sama da kuma dusar kankara da ba safai a kan ganin irinsu ba a yankunan da ke kudancin kasar Sin, ta haka larduna fiye da 10 sun gamu da bala'in bisa matsayi daban daban, mutane fiye da 60 sun mutu, yawan hasara da aka samu kai tsaye a fannin tattalin arziki ya kai kusan kudin Sin Yuan biliyan 54. Bayan faruwar bala'in, bangarori daban daban sun gudanar da ayyukan ceto cikin gaggawa, kuma yanzu an riga an farfado da zaman jama'a da ayyukan samarwa na yankuna masu fama da bala'in.

Zhou Hongren, mataimakin shugaban hukumar gudanar da tattalin arziki ta kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, ko da yake an samu hasara sakamakon bala'in dusar kankara, amma a galibi dai, ba zai yi illa sosai ga tatalin arzikin kasar Sin ba, haka kuma ba zai canja kyakkyawar makomar raya tattalin arzikin Sin ba. Kuma ya kara da cewa,

"wasu yankunan da ke kudancin kasar Sin ne kawai suka gamu da bala'in dusar kankara, shi ya sa bala'in ba zai yi illa sosai ga duk fadin kasar ba. A waje daya kuma, ana kasancewa da abubuwa masu kyau wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki. Alal misali, kasar Sin za ta yi gasar wasannin Olympics a shekarar nan, kuma dukkan Sinawa na cike da imani sosai gare ta. Bugu da kari kuma, ana gudanar da ayyukan samarwa kamar yadda ya kamata a wurare daban daban na kasar Sin lokacin da ake fama da bala'in. Sabo da haka, mun yanke shawarar da muka ambata a baya."

Haka kuma, Han Meng, wani kwararre wajen tattalin arziki na cibiyar binciken kimiyyar al'umma ta kasar Sin yana da ra'ayi iri daya tare da Mr. Zhu. Kuma ya bayyana cewa,

"Wannan bala'in dusar kankara ba zai yi illa sosai ga tattalin arzikin kasar Sin ba, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a 'yan shekarun nan da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu saurin karuwa ba tare da tangarda ba, jimlar GDP ta kasar Sin kuwa ta karu sosai, yawan kudaden shiga da jama'ar Sin suka samu yana ta karuwa, kuma an gudanar da odar tattalin arziki kamar yadda ya kamata, haka kuma hatsi ya yi girbi mai armashi a jerin shekaru hudu da suka gabata."

An labarta cewa, bisa aikin ceto da ake gudanarwa a wurera daban daban masu fama da bala'in dusar kankara yadda ya kamata, ya zuwa yanzu an riga an kusan farfado da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki da zirga-zirga na yankuna masu fama da bala'i, kuma an ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a masu fama da bala'in.

Mr. Han ya nuna cewa, sabo da a 'yan shekarun nan da suka gabata, yawan bala'u daga indallahi da suka faru ya samu karuwa, shi ya sa ya kamata kasashe daban daban su yi kokari tare wajen fuskantar matsalar muhallin halittu. Kuma kamata ya yi kasar Sin ta tsamo darasi daga wannan bala'in dusar kankara domin gudanar da ayyukan ceto na nan gaba. Kuma ya kara da cewa,

"ya kamata a yi la'akari sosai a fannoni makamashi da muhimman ayyukan yau da kullum na masana'antu da na birane da kuma muhimman matakan shawo kan bala'i daga indallahi, ta yadda za a iya samun wani cikakken tsari da kuma matakan ko ta kwana domin yin rigakafi kafin faruwar bala'i."(Kande Gao)