Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 16:21:34    
Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa a bikin bazara

cri

Bikin bazara wani biki ne mafi muhimmanci ga Sinawa. A lokacin bikin bazara, fararen hula na kasar Sin sun fi sha'awar halartar bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin. Kullum a kan shirya irin wadannan bukukuwa a gidajen ibada ko kuma wuraren yawon shakatawa, inda ake iya yin harkokin nishadi da yawon shakatawa da kuma saye-saye. Sa'an nan kuma, bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen nuna al'adun gargajiya na kasar Sin. A matsayinsa na wani birni na al'ada mai dogon tarihi, birnin Beijing ya fi shahara bisa wadannan bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya. A cikin shirinmu na yau, za mu zagaye a wannan birni domin halartar bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya tare, mun yi imani da cewa, tabbas ne za ku kara saninku.

Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na Beijing sun yi kama da lunguna da kuma gidaje masu tsakar gida irin na gargajiya a Beijing, dukkansu alamu ne na wannan birni ta fuskar tarihi. An ce, an fara shirya bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a nan Beijing yau da shekaru dubu 1 ko fiye. Asalinsu harkokin sadaukarwa ne da aka yi domin addini, amma a lokacin da ake yin harkokin sadaukarwa, an kuma gudanar da wasu harkokin kasuwanci. Sannu a hankali bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin na yanzu sun zama wani wurin da mutane suka sake saduwa da juna da kuma yin saye-saye a lokacin bikin bazara.

Bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da aka yi a wurin yawon shakatawa na Ditan na daya daga cikin irin wadannan bukukuwa a nan Beijing. A kan yi harkokin nishadi na gargajiya da dimbin fararen hula suke nuna sha'awa a kai. An gina wurin yawon shakatawa na Ditan a shekarar 1530, fadinsa ya wuce kadada 40, shi ne wurin da sarakunan gargajiya su kan yi bikin sadaukarwa domin nuna girmamawa ga kasa. Zhang Jinsong, wani jami'in kwamitin shirya bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya yi mana karin bayani cewe, a shekarun baya, yawan masu yawon shakatawa da suka halarci bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya kai misalin miliya 1 a ko wace shekara. Karin masu yawon shakatawa da suka zo daga sauran wuraren kasar Sin har ma daga ketare sun mai da hankulansu kan yanayin musamman da aka samu a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan. Ya gaya mana cewa,

'Ma iya cewa, bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya janyo hankulan masu yawon shakatawa masu tarin yawa daga sauran wuraren kasar Sin da kuma kasashen ketare domin sun iya kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya na kasar Sin a zamanin yanzu. A cikin wannan kyakkyawan wurin yawon shakatawa, a tsakanin gine-ginen gargajiya na kasar Sin, musamman ma baki na iya ganin dimbin mutane da kayayyaki iri daban daban da abinci iri daban daban da kuma kallon harkokin al'adu masu ban sha'awa.'

Za a yi bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan tun daga ran 6 zuwa ran 13 ga wata. Za a nuna sigar musamman ta tsarin gine-gine na titunan Beijing, wato katangu da fale-falen burki da jinka masu launin toka-toka, ta haka mutane za su iya yawo a cikin lungunan gargajiya na Beijing a zamanin da. A lokacin da ake yin wannan biki, za a nuna wasannin kwaikwayo game da aikin sadaukarwa a ko wace rana da safe a nan. Ta haka, masu yawon shakatawa za su iya ganin yadda sarakunan zamanin daular Qing na kasar Sin suka yi bikin sadaukarwa domin neman tabbatar da kwanciyar hankali a kasar Sin da kuma yin girbi mai armashi da kuma samun yanayi mai kyau yau da shekaru fiye da 100. Ban da wannan kuma, sun iya kara saninsu kan al'adun gargajiya da yawa da mazauna Beijing suka bi a zamanin da.

Shekarar bana, shekara ce ta bera, wato bera ta zama alamarta a kasar Sin. shi ya sa hukumar shirya bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ta kera abubuwan nuna fatan alheri masu nuna sigar musamman ta shekarar Bera, wato kyawawan mutum-mutumi na beraye 2 da aka yi da tabo, za a sayar da su kadan. Wadannan kyawawan beraye 2 masu launin ja da na rawaye sun sa hannunsu a baya, sun daga kansu. A lokacin bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya, za su yi maraba da masu yawon shakatawa daga wurare daban daban cikin murmushi. Kazalika kuma, saboda za a yi gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara, shi ya sa za a bayyana alamun wasannin Olympic a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan. Zhang Jinsong ya yi mana karin bayani cewa, 'Za a yi gasar wasannin Olympic a nan Beijing a wannan shekara. Unguwar Dongcheng unguwa ce daya kacal daga cikin unguwanni 4 na yankin tsakiya na Beijing da za a yi shirye-shiryen gasars wasannin Olympic, wato shirin wasan dambe. Za mu fito da dandamalin kara fahimta kan wasan dambe, ta haka mutane za su fahimci yanayin gasanni kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Masu yawon shakatawa za su iya samun aikin horaswa daga 'yan wasan dambe, za su kuma iya yin takara da su.'

1 2