Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili mai farin jini na "wakoki masu karbuwa a ko'ina a kasar Sin", ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin. Bayan kwanaki uku, za mu shiga wata sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. Shi ya sa da farko, ina son in taya wa dukkan masu sauraronmu murnar sabuwar shekara, kuma ina fatan za ku kasance cikin koshin lafiya da alheri a cikin wannan shekara. A waje daya kuma ina fatan shirinmu na yau da na shirya musamman don bikin bazara wato sabuwar shekara bisa kalandar gargarjiyar kasar Sin zai faranta muku zuciya sosai.
Bikin bazara biki ne mafi muhimmanci ga fararen hula na kasar Sin. A cikin dubban shekaru da suka gabata, in bikin bazara ya zo, to tabbas ne mutane za su taya murnar bikin tare da wake-wake da raye-raye. To, a cikin shirinmu na yau, zan gayyaci wasu shahararrun mawakan kasar Sin don kawo wa masu sauraronmu fatan alheri. Na farko shi ne wata kungiyar wake-wake irin na salon Rock da ake kiranta "mutane masu siriri", kuma sunan wakar da ta kawo mana shi ne "sabuwar shekara". A cikin wakar, mawaka sun bayyana fatan alheri da burinsu na sabuwar shekra bisa muryarsu mai matukar karfi. To, yanzu bari mu saurari wakar.
Ranar bikin bazara ita ce ranar farko ta sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kuma a kan kira ta "Nian" a bakin Sinawa. Sabo da a kan dora matukar muhimmanci kan bikin, shi ya sa a kan shirya harkoki iri daban dabn bisa al'adun gargajiya na kasar Sin. Kafin zuwan bikin bazara, tabbas ne a tsabtace gidansa da kuma wanke kayayyakin gida iri iri. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ana son share dukkan abubuwa marasa kyau kafin zuwan sabuwar shekara. To, yanzu Li Yuchun, wata zabiya ta kasar Sin da na gayyaci za ta kawo mana wata waka mai dadin ji don taya murnar sabuwar shekara, wadda ake kiranta "jin dadi a ko wace awa".
A cikin al'adun gargajiya na kasar Sin wajen taya murnar bikin bazara, bai wa juna fatan alheri wata hanya ce da ba a iya raba ta ba. A ranar farko ta sabuwar shekara, a kan tashi da sassafe, da kuma sanya tufafi mafi kyaun gani don kai wa 'yan iyalai da abokai ziyara da kuma ba su fatan alheri. Ana fatan tsoffaffi za su samu koshin lafiya, kuma yara za su samu girma lami lafiya. Haka kuma a kan fatan abokai za su iya samun watada a cikin sabuwar shekara. To, yanzu bari mu saurari fatan alherin da Liu Dehua, wani mawakin shiyyar HongKong ta kasar Sin da ya shahara kwarai da gaske ya kai muku, wato "samun kudi a sabuwar shekara".
A kan yi buri da yawa a cikin zaman rayuwar wani mutum. Shekara da shekaru, buri ya samar da haske ga zaman rayuwa na yau da kullum. Tare da zuwan sabuwar shekara, wasu abubuwan da ba a iya mantawa ba sun wuce, amma abubuwa mafi kyau suna jiranmu. Sabo da haka, a wannan lokaci, ko wane mutumin da ke da buri ya riga ya tsara shiri don jin dadin zaman rayuwarsa. Shi ya sa ina fatan dukkan masu sauraronmu za ku iya cimma burinsu a cikin wannan sabuwar shekara. To, yanzu bari mu saurari burin Hu Yanbin a wannan sabuwar shekara ta wakarsa.
Haka kuma bikin bazara wani biki ne da dukkan membobin iyali suke haduwa. Game da mutanen da suka bar gida don karatu ko aiki, komin nesa, tabbas ne su kan koma gida don su yi bikin bazara tare da iyalansu. Gargadin da iyaye suke yi wa yaransu, da kuma gaisuwa tsakanin 'yan iyali za su raka wadanda suka bar gida don aiki a cikin zaman rayuwarsu. To yanzu bari mu saurari wata wakar da Long Meizi ta rera mai taken "koma gida don yin bikin bazara ko da kake da kudi ko maras kudi". Kuma ina fatan masu sauraronmu masu cin rani za ku iya koma gida kullum don hadu da iyayenku da matanku da kuma yaranku.
Yanzu a lokacin bikin bazara, wasu mutane suna son haduwa da 'yan iyali tare a gida, amma wasu kuwa suna son yawon shakatawa tare da 'yan iyali da abokai. Game da matasa, su kan sha aiki sosai, kuma ba safai su kan kwashe yawan lokuta wajen yawon shakatawa tare da abokai ba, shi ya sa bikin bazara na kwanaki 7 ya ba su wata kyakkyawar dama. Ta haka ba kawai suna iya rage damuwar aiki ba, har ma suna iya jin dadin zaman rayuwarsu. To, yanzu bari mu sha iska tare da zakin muryar Cai Chunjia, wata Basiniya yar kaka gida ta kasar Singapore.
A sabuwar shekara, muna fatan za a iya samun zaman lafiya a duk duniya, jama'ar kasashe daban daban za su iya samun alheri da kuma jin dadin zaman rayuwarsu. To, a karshen shirinmu na yau, bari mu saurari wata wakar da wasu mawakan kasar Sin suka rera tare mai taken "buri", wadda ta bayyana burin Sinawa na fatan samun zaman lafiya a duniya.
To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na "wakoki masu karbuwa a ko'ina a kasar Sin" ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa barka da sabuwar shekara da kuma a kansace lafiya.(Kande Gao)
|