Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 08:35:38    
Kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen jigilar kwal da man fetur da wutar lantarki

cri

Ya zuwa yanzu kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen jigilar kwal da man fetur da wutar lantaki domin tabbatar da fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara. Yanzu halin da ake ciki dangane da karancin kwal da zirga-zirga da wutar lantarki da man fetur a wasu yankunan kasar ya riga ya samu sassauci.

Ya zuwa ran 4 ga wata da safe, motoci fiye da dubu 6 da aka tsayar da su a lardunan Guangdong da Hunan duka sun kama kan hanya. Wannan ya almanta cewa, tagwayen hanyar mota da ke tsakanin birnin Beijing da birnin Zhuhai, wato wata muhimmiyar tagwayen hanya da ke hada arewa da kudancin kasar ta sake komawa aike da zirga-zirga kamar yadda ya kamata. A waje daya kuma, ban da wasu kananan filayen saukar jiragen sama wadanda ba su da injin kawar da kankara, an riga an bude sauran filayen saukar jiragen sama na fasinja gaba daya. Zango na kudancin hanyar dogo da ke tsakanin Beijing da Guangzhou da hanyar dogo da ke tsakanin Shanghai da Kunming sun kuma soma koma yadda ya kamata wajen sufurin kayayyaki da fasinjoji.

Bugu da kari kuma, galibin tsare-tsaren jigilar wutar lantarki sun koma yadda ya kamata. Haka kuma, tsarin sadarwa suna aiki kamar yadda ya kamata. Sannan kuma, aikin samar da kwal da man fetur yana ta samun kyautatuwa a yankunan da ke fama da bala'in ruwan sama da dusar kantara. (Sanusi Chen)