Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 15:23:04    
Cibiyar taruruka ta kasar Sin

cri

Masu karatu, a cikin wurin shakatawa na gandun daji na wasannin Olympic na Beijing da ake samun dimbin bishiyoyi, akwai wani babban gini mai fadin kadada 12, wanda kuma fadin ginin da ake amfani ya kai murabba'in mita dubu 500 ko fiye, shi ne cibiyar taruruka ta kasar Sin, inda za a yi shirin wasan takobi na gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar bana.

Cibiyar taruruka ta kasar Sin dakin wasa na wucin gadi ne ga gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ta hada da wani babban gini da ote-otel guda 2 da kuma gine-ginen ofis guda 2. Shi ne gini mafi girma a cikin dukkan gine-ginen wasannin Olympic.

A lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a raba muhimmin gini na wannan cibiya zuwa sassa 2, wato bangare na kudu da na arewa. Za a yi kwaskwarima kan bangare na kudu zuwa dakin wasa domin yin shirin wasan takobi da shirin wasan Pentathlon na zamani na gasar wasannin Olympic. Sa'an nan kuma, za a mayar da bangare na arewa a matsayin cibiyar rediyo ta kasa da kasa wato IBC a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing domin bai wa abokanmu manema labaru na wurare daban daban na duniya hidima.

Fadin dakin wasan takobi ya kai misalin murabba'in mota dubu 56. 'Yan wasa za su iya samun aikin horaswa kafin gasa a cikin dakin wasa na horaswa da dakin motsa jini da ke bene na 1 da na 2 da na 3. Za a yi shirin wasan takobi na gasar wasannin Olympic ta Beijing a bene na 4. Akwai hanyoyin gasa 4 a wurin gasa, tare da kujerun 'yan kallo kusan dubu 6. Bayan kawo karshen shirin wasan takobi, za a yi sassa 2 na wasan Pentathlon na zamani. A lokacin, za a yi kwaskwarima kan wannan wurin gasa zuwa wurin gasa mai hanyoyin gasa 10 da wuraren harbi 38 tare kuma da kujerun 'yan kallo fiye da dubu 4.

Cibiyar IBC kuwa, fadinta ya kai misalin murabba'in mita dubu 47. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a ba da hidima ga manema labaru na talibijin kimanin dubu 16 da suka yi rajista. Ta haka za a watsa shirye-shirye daga dukkan fannoni kan dukkan shirye-shiryen gasar wasannin Olympic ta Beijing zuwa ko ina a duniya.

A matsayinsa na dakin wasa na wucin gadi, za a lalata dakin wasan takobi bayan gasar wasannin Olympic. Za a yi kwaskwarima kan wurin gasa na bene na 4 zuwa wani babban zauren taro mai daukar mutane dubu 6. Za a kafa tsarin kira taruruka ta hanyar talibijin na zamani a babban zauren, ta haka, wannan cibiya za ta zama babbar cibiyar taruruka a Beijing, inda za a yi tarurukan kasa da kasa da kuma tarurukan nune-nune.

Abin ya cancanci a bayyana, shi ne bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a gina wani lambun shan iska a waje da cibiyar taruruka ta kasar Sin, wanda kuma ya yi kasa da doron kasa har da mita 7. Ta haka, cibiyar taruruka ta kasar Sin za ta kasance babban gini mai ba da hidima ta fuskar kira taruruka da tarurukan nune-nune da otel-otel da harkokin kasuwanci da nishadi, mazaunan Beijing za su sami wani wuri daban domin yin nishadi da yawon shakatawa.