Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-05 11:04:09    
Shugabanni da kafofin watsa labarai na kasashen waje sun nuna yabo ga kokarin da Sin ke yi wajen fama da bala'in dusar kankara

cri
A ran 4 ga wata, shugabannin kasashen Habasha da Japan da kuma kungiyar tarayyar kasashen Larabawa sun nuna jaje ga wasu yankunan kasar Sin da ke fama da bala'in dusar kankara mai tsanani, kuma sun yi imanin cewa, tabbas ne kasar Sin za ta ci nasara a cikin wannan yakin da bala'in dusar kankara.

A waje daya kuma, kafofin watsa labarai na kasashen Amurka da Korea ta Kudu da Pakistan da dai sauransu sun nuna yabo sosai ga kokarin da gwamnati da jama'ar Sin ke yi wajen fama da bala'in.

Lokacin da ministan harkokin waje na kasar Habasha Seyoum Mesfin ke ganawa da jakadan Sin da ke kasar Lin Lin, ya bayyana tausayi da jaje da firayim minista Meles Zenawi na Habasha ya nuna wa firayim minista Wen Jiabao da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi. Kuma ya ce, kasar Habasha ta yi imanin cewa, dole ne jama'ar Sin za su iya haye wahaloli da kuma cimma nasara a cikin aikin fama da bala'in dusar kankara a karkashin jagorancin gwamnatin Sin.(Kande Gao)