Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-04 19:12:10    
Gwamnatin kasar Sin na kokarin kyautata rayuwar jama'a da kuma inganta jituwa na zamantakewar al'ummar kasar

cri

A 'yan shekarun baya dai, gwamnatin kasar Sin ta yi la'akari da hakikanan abubuwan da jama'ar kasar suka fi mai da hankali a kai, har ta fito da wasu jerin manufofi na game da aikin jinya, da aikin bada kudin fensho, da bada ilimi da kuma na samar da gidajen kwana da dai sauransu da zummar kyautata yanayin jinya domin jama'a, da kara yawan kudin fensho domin tsofaffi, da bada ilimi a fayu domin 'yan makarantun firamare da na sakandare da kuma bada tabbaci ga samar da gidajen kwana domin iyalai marasa galihu. Wadannan matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun kyautata rayuwar jama'ar kasar da kuma inganta jituwa na zamantakewar al'ummar kasar.

Game da batun rashin samun saukin ganin likita da kuma sayan magunguna masu tsada dake addabar wasu wuraren kasar, gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin kafa cikakken tsarin yin jinya a unguwa-unguwa na yankin kasar. Alal misali : a birnin Nanchang na larldin Jiangxi dake tsakiyar kasar Sin, tuni a shekarar 2007, aka kafa hukumomin jinya kimanin 300, inda mazauna wurin suke iya ganin likita cikin minti 15 kawai idan sun yi tafiya da kafa daga gidajensu. Wani dan birnin Nanchang mai suna Fang Wen ya fada wa wakilinmu cewa : "Na kan kashe minti biyu ko uku kawai wajen zuwan tashar kiwon lafiya ta unguwa don ganin likita, inda ake yin hidimomi da kyau. Idan na bugu musu wayar tarho, to likitan tashar yakan zo gidana don yin jiyya".

Jama'a masu saurare, domin tabbatar da burin dake cewa: " Kowa da kowa na da ikon more tsarin samun jinya bisa tushe", tun daga shekarar da ta gabata ne, gwamnatin kasar Sin ta yi namijin kokari wajen yin gwaje-gwajen bada tabbaci ga yin jinya bisa tushe ga mazauna birane da garuruwa na dukkan fadin kasar, inda akwai mutane sama da miliyan dari biyu da arba'in, wadanda ba su da aikin yi. Bisa abubuwan da aka tanada, an ce, 'yan makaranta, da yara kanana da kuma sauran mazauna birane da na garuruwa wadanda ba su da aikin yi, dukkansu su iya shiga tsarin bada tabbaci ga samun jinya bisa son ransu. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan mutanen da suka shiga irin wannan kyakkyawan tsari ya dara miliyan 40. Sassan kula da harkokin bada tabbaci a fannin kwadago na kasar Sin sun fito da shawarar yadada wuraren gwaje-gwaje da kashi 50 cikin kashi 100 a fannin bada tabbaci ga samun jinya a birane da garuruwan kasar; Ban da wannan kuma, za a ci gaba da gudanar da tsarin hadin gwiwa irin na sabon salo a fannin jinya a kauyukan kasar. An labarta cewa, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar bara, yawan mutanen dukkan fadin kasar da suka shiga irin wannan sabon tsarin jinya ya kai miliyan dari bakwai da ashirin da shida.

Kawo wa tsofaffi zaman jin dadi, wani batu ne daban da gwamnatin kasar Sin ta fi mai da hankali a kai. Yanzu a kasar Sin, akwai ma'aikata sama da miliyan arba'in da suka yi ritaya, wadanda kudi kalilai ne suke samu. To, domin bada kariya ga rayuwarsu, a 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta ba su karin kudin fensho ba sau daya ba sau biyu ba. Mr. Yin Chengji, mai magana da yawun ma'aikatar kwadago mai kula da harkokin bada tabbaci ga zamantakewar al'ummar kasar Sin ya furta cewa : ' Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yanke shawarar cewa, tun daga shekarar da muke ciki zuwa shekarar 2010, gwamnatin kasar za ta ci gaba da kara bai wa ma'aikatan da suka yi ritaya kudin fensho. Ana sa ran kowane ma'aikacin da ya yi ritaya zai iya samun kudin fensho fiye da Yuan 1,200 a kowane wata a shekarar 2010.'

A waje daya kuma, an gudanar da tsarin bada ilimi a fayu lami-lafiya a kauyukan kasar a shekarar da ta gabata. 'Yan makarantun firamare da na sakandare da suka kai miliyan dari da hamsin na dukkan fadin kasar sun ci gajiyar lamarin. Wata budurwa mai suna Fu Qin dake da shekaru 15 da haihuwa daga wani kauye ta yi farin ciki matuka da fadin cewa : 'Yanzu haka dai, gwamnati ta kaddamar da dimbin kyawawan manufofi. Hakan ya ba ni damar yin karatu a birnin Chengdu daga can wani kauye mai nisa yayin da nake biyo iyayenmu zuwan birnin domin yin aikin ci rani'. ( Sani Wang )