---- Bisa kokarin da hukumomin binciken yanayin kasa na kasar Sin suka yi cikin shekaru 4 da suka wuce, an gano albarkatun kwal wadanda yawansu ya kai ton biliyan 164 a shekarar bara a babban kwarin kasa mai suna Zhundong da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, adadin nan ya ninka sau 1.65 bisa na shekarar 2003.
Daga shekarar 2004, babbar kungiyar binciken yanayin kasa ta 9 ta hukumar ma'adinan jihar Xinjiang ta fara aikin safiyon albarkatun kwal a filin hakar kwal na Zhundong, ya zuwa karshen shekarar da ta wuce, yawan albarkatun kwal da ta gano ya kai ton biliyan 164, wato an gano manyan filayen kwal 11, daga cikinsu da akwai mahakan kwai na sarari guda 3. Yawan albarkatun kwal da aka binciko daga mahakar kwal ta Zhundong Dajing da Jiangjunmiao ta rukunin Luneng ya kai ton biliyan 33.4, wato ta zama mahakar kwal da ke da albarkatun kwal mafi yawa ta kasar Sin.
|