Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-02 21:20:50    
Mutane fiye da miliyan 77 na kasar Sin suna fama da bala'in dusar kankara

cri

Wakilinmu ya samu labari daga ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, cewa ya zuwa ran 28 ga wata da karfe 2 da yamma, ruwan sama da dusar kankara da aka yi daga ran 10 ga wata sun riga sun yi sanadiyar mutuwar Sinawa 24 yayin da mutane fiye da miliyan 77.86 suke fama da su.

Haka kuma bisa kididdigar da ma'aikatar ta bayar, an ce, larduna da jihohi masu cin gashin kai 14 na kasar Sin ciki har da Hunan da Hubei da Guzhou da kuma Shanxi suna fama da bala'in. Kuma bayan faruwar bala'in, ma'aikatar ta kaddamar da shirin ko ta kwana nan da nan. Ya zuwa yanzu, an riga an tsugunar da mutane fiye da dubu 350.

A waje daya kuma, wakilinmu ya samu labarin cewa, a wasu wuraren da ke fama da dusar kankara, yawan farashin kayayyaki ya samu karuwa a bayyane sakamakon mumunen yanayi. Yanzu daya bayan daya biranen da ke karkarshin jagorancin gwamnatin Sin kai tsaye da larduna da kuma jihohi masu cin gashin kai fiye da 20 sun riga sun dauki matakai wajen sa baki a kan farashin kayayyaki cikin gajeren lokaci.(Kande Gao)