Beijing zai kara sa ido kan ingancin abincin da ake shigowa da su, musamman ma kan aikin binciken abincin da za a samar da su ga wasannin Olympic, kuma idan abincin ba su iya biyan bukata ba, za a mai da su ko a lalata su.
An sami wannan labari ne a gun taron tabbatar da ingancin abinci mai inganci na Beijing da aka yi. Mr. Zhang Zhikuan direkatan ofishin kula da ingancin abinci na Beijing ya ce, za a fara tafiyar da tsarin bincike da sa ido kan ingancin abinci na Wasannin Olympic da za a yi a Beijing a shekarar da muke ciki, da tsarin rajista danyen kayan abinci, da tsarin ajiye samfurin abinci, da tsarin binciken ingancin abinci, da tsarin binciken asalin abinci.
|