Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-01 20:34:05    
An rufe manyan masana'antu 10 a kasar Sin domin tabbatar da ingancin iska

cri
Birnin Beijing da birnin Tianjin da lardin Hebei da suke kewayen birnin Beijing sun riga sun rufe manyan masana'antu 10 wadanda suke gurbata muhalli domin tabbatar da ingancin iska a lokacin da ake shirya gasar wasanin motsa jiki ta Olympics a karo na 29 a nan birnin Beijing a lokacin zafi na shekarar 2008.

Rukunin daidaita aikin tabbatar da ingancin iska da ke karkashin kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olynmpics ta Beijing ya bayar da wannan labari a ran 1 ga watan Faburairu.

An labarta cewa, ya zuwa yanzu, wannan aikin tabbatar da ingancin iska yana shafar birnin Beijing da na Tianjin da lardunan Hebei da Shanxi da jihar Mongoliya ta gida mai cin gabashin kanta da lardin Shandong wadanda suke kusa da birnin Beijing. Jami'an hukumomin tabbatar da ingancin muhalli na wadannan yankuna 6 sun bayyana cewa, za su ci gaba da daukan matakai iri daban-daban bisa shirin tabbatar da ingancin iska domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics, kuma za su ci gaba da rufe masana'antu wadanda suke gurbata muhalli sosai. (Sanusi Chen)