Aminai 'yan Afrika, bayan da aka yi aiki tukuru na tsawon watanni kimanin shida, sai aka kawo karshen aikin zaben mutane masu daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a wurare daban-daban na kasar Sin a karshen shekarar da ta gabata. Yawan wadanda aka zabe su don su zama masu daukar wutar yula ya kai 11,534. A cikin shirinmu na yau dai, za mu dan gutsura muku wani bayani kan wani ma'aikaci dan cin rani kuma dan takarar daukar wutar yula. Sunansa Zhou Guoyun, daya daga cikin wadannan 'yan takarar zama masu daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.
A ranar 1 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, shi Zhou Guoyun, wanda shi ne nagartaccen dan kwadago na kasar Sin, ya samu wayar tarho daga aminansa da kuma dangoginsa yayin da yake shiga aikin gina filin wasannin Olympics mai siffar gidan tsuntsaye wato " Bird's net" a Turance. Wannan filin wasanni, muhimmin filin wasanni ne na gasar wasannin Olympics ta Beijing. A cikin wayar tarhon, sun taya shi murna saboda gwamnatin birnin Beijing ta bayyana sunansa a hukumance a matsayin wani mai daukar wutar yula ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008.
Mr. Zhou Guoyun ya zo ne daga kauyen Zhou Tan na gundumar Hua ta lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin. Shekaru sama da 20 ke nan yake yin aikin kwadago a nan birnin Beijing. A shekarar 2003, ya samu damar shiga aikin gina filin wasannin Olympics mai siffar gidan tsuntsaye wato " Bird's Net". Yanzu, ana kusan kammala gina shi. Mr. Zhou ya yi farin ciki matuka da fadin cewa " A matsayin wani kamfani dake daukar nauyin gina filin wasannin, musamman ma, mu mutane na wannan zuriya, lallai mun yi alfarmar samun damar shiga harkokin gudanar da gagarumar gasar wasannin Olympics".
Wani jami'in cibiyar kular da harkokin daular wutar yula ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympics wato BOCOG ya fada wa wakilinmu cewa, shi Zhou Guoyun mai shekaru 43 da haihuwa ya zo nan Birnin Beijing domin yin aikin kwadago bayan da ya sha kaye a jarrabawar shiga jami'a da aka gudanar a shekarar 1984. A matsayin wani ma'aikaci dan cin rani, Mr. Zhou Guoyun ba ya so a tafi an bar shi baya wajen aiki, inda har kullum yake himmantuwa wajen koyon fasahohin sana'a a fannin gine-gine, har ya shiga sahun gaba na nagartattun 'yan cin rani. Hakan ya samar masa da kyakkyawar damar shiga ayyukan gina ginin cibiyar sabon karni ta kasar Sin, da babban dakin nuna wasannin kwaikwayo da kuma muhimmin filin wasannin motsa jiki mai siffar gidan tsuntsaye wato Bird's Net da dai sauran ire-iren gine-gine fiye da 160.
Jama'a masu sauraro, tun daga shekarar 2003 ne, Mr. Zhou Guoyun ya jagoranci 'yan kungiyar barade wadda aka lakaba mata da sunansa na kansa wajen shiga aikin gina filin wasa mai siffar Bird's Net, da dakin wasannin motsa jiki na kasar Sin da kuma kauyen 'yan wasa na Olympics da dai sauran gine-gine, wadanda gaba dayansu suka samu babban yabo daga kwararru a fannin gine-gine na gida da na waje. Mr. Zhou ya gwada takardar yabo a gaban wakilinmu, yana kuma mai cewa: " Wannan dai takardar yabo ce ta farko da na samu a cikin aikin gina filin wasa mai siffar gidan tsuntsaye wato Bird's Net na Olympics. Lallai ina darajanta ta kwarai da gaske".
Da yake Mr. Zhou Guoyun ya yi fitaccen aiki, shi ya sa ya sau lambobi masu daukaka da dama kamar na daya daga cikin nagartattun samari 'yan cin rani guda 10 na kasar Sin, da dan kwadago mai bada misali na duk kasar da kuma nagartaccen ma'aikacin gina ayyukan wasannin Olympics da dai sauransu. ( Sani Wang )
|