A kwanan nan, ofishoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen Korea ta Kudu da Uruguay da Mauritius da Sweden da kuma Uganda sun shirya liyafar bikin bazara bi da bi domin taya murnar zuwan sabuwar shekara ta 2008 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.
Jakadan Sin da ke kasar Mauritius Gao Yuchen ya yi jawabi a cikin liyafar bikin bazara da aka yi a ran 31 ga watan Janairu, cewa a cikin shekarar da ta gabata, Sinawa 'yan kaka gida da ke kasar Mauritius sun kafa kungiyar sa kaimi ga aikin dinkuwar kasar Sin gaba daya cikin lumana, da kuma bayyana kudurinsu wajen kin amincewa da neman 'yancin kan Taiwan da kuma dukufa kan samun dinkuwar kasar Sin gaba daya.
Haka kuma ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Uganda ya yi liyafar bikin bazara a birnin Kampala, babban birnin kasar a ran 31 ga watan jiya, inda jakada Sun Heping ya ba da jawabin cewa, a shekara ta 2007, an raya dangantakar aminci da ke tsakanin Sin da Uganda daga dukkan fannoni kamar yadda ya kamata, kuma bangarorin biyu sun samu sakamako mai kyau wajen hadin kansu a fannoni daban daban.(Kande Gao)
|