Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-31 18:45:27    
Kasar Sin za ta kara raya ayyukan yau da kullum na aikin gona

cri
A ran 30 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua, wato wani kamfanin dillancin labaru na gwamnatin kasar Sin ta bayar da takarda mai lamba farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda aka nuna cewa, za a kara raya ayyukan yau da kullum na aikin gona da sa kaimi wajen raya aikin gona da karuwar yawan kudin shiga na manoma. A waje daya kuma, za a tabbatar da samar da isashen amfanin gona da daidaita batutuwan zaman rayuwar manoma yadda ya kamata. A ran 31 ga wata, Mr. Chen Xiwen, mataimakin direktan ofishin kungiyar ba da jagoranci kan ayyukan kudi da tattalin arziki ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar wannan ne takarda mai lamban farko da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayar a karo na biyar game da batutuwa 3, wato batun aikin gona da na kauyuka da na manoma a cikin jerin shekaru 5 da suka wuce. Wannan kuma ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wadannan batutuwa 3. Mr. Chen ya ce, "A hakika dai, kasar Sin tana samun bunkasuwar aikin gona da kyau yanzu, amma tana kuma fuskantar matsaloli masu tsanani da dama. Matsala mafi tsanani daga cikinsu ita ce, ayyukan yau da kullum na aikin gona ba su da gindi sosai. Idan ana son tabbatar da bunkasar aikin gona na kasar Sin cikin hali mai dorewa ba tare da tangarda ba, da kuma biyan bukatun amfanin gona da ake bukata a kasuwa da kuma kara yawan kudin shiga da manoma suke samu, dole ne a kara kyautata ayyukan yau da kullum na aikin gona da karfafa matsayin aikin gona cikin tattalin arzikin kasar Sin. A waje daya kuma, dole ne a yi kokarin kara yawan hatsin da ake nema a kowane hekta."

Tun daga shekara ta 2004, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi ta bayar da takardarta mai lamba farko game da aikin gona da kauyuka da manoma domin kokarin sassauta gibin da ke kasancewa a birane da kauyuka da kuma kokarin kara yawan kudin shiga da manoma suke samu da tabbatar da samar da isassun hatsin da ake nema.

Mr. Chen ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, lokacin da ake fama da bala'u daga indallahi iri daban-daban a nan kasar Sin, aikin gona na kasar ya samu cigaba mai dorewa. Jimlar kudaden aikin gona da aka samu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2891, jimlar hatsin da kasar Sin ta samu ya kai fiye da kilo biliyan dari 5. Amma domin muhalllin halittu ya kara yin tsanani, yawan amfanin gona bai iya biyan bukatun da ake nema a kasuwa ba. A waje daya kuma, kasuwannin kasa da kasa suna kawo tasiri ga aikin gona na kasar Sin sosai. Kuma ba a zuba isashen kudi kan ayyukan yau da kullum na aikin gona ba. Sabo da haka, cikin gaggawa ne an nemi gwamnatin kasar Sin da ta kara raya ayyukan yau da kullum na aikin gona. Mr. Chen ya ce, "Yawan karin kudaden da kasar Sin ta kebe daga baitulmalin tsakiya domin batutuwan aikin gona da kauyuka da manomaya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 80 a shekarar da ta gabata. Ko da yake yanzu ana jiran za a tabbatar da yawan kudaden da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta zuba kan ayyukan gona da kauyuka da manoma a shekarar 2008 a gun babban taron wakilan jama'ar duk kasar Sin. Amma na samu labari cewa, yawan karin kudade zai wuce na shekarar 2007, wato zai wuce kudin Renminbi yuan biliyan dari 1."

An labarta cewa, za a yi amfani da galibin kudaden da gwamnatin tsakiya za ta kebe wa aikin gona kan ayyukan yau da kullumna aikin gona, musamman kan kananan ayyukan ruwa. A waje daya kuma, za a samar da karin kudin tallafi ga manoma wadanda suke aikin gona. Sannan kuma za a kara zuba kudade kan ayyukan samar da ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin mota da man gas wadanda suke da nasaba da zaman rayuwar manoma domin kyautata ingancin zaman rayuwarsu.