Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-30 21:39:48    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(24/01-30/01)

cri
Ran 21 ga wata, rana ce da ta rage sauran kwanaki 200 da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing. A wannan rana, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kaddamar da aikin yada wakokin wasannin Olympic a hukunce. A cikin kwanaki 200 masu zuwa da kuma lokacin gasar wasannin Olympic, za a yada wakokin wasannin Olympic ta gidajen talibiji da gidajen rediyo da wayoyin salula na duk kasar Sin. A karshen watanni 6 na wannan sheakra, za a kaddamar da wakar da ke nuna muhimmancin gasar wasannin Olympic ta Beijing a hukunce. Tun daga shekarar 2003, aka fara tattara wakokin gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma za a kammala wannan aiki a watan Maris na wannan shekara. Yanzu an riga an tattara wakoki fiye da dubu 3, sa'an nan kuma, masu kide-kide fiye da dubu 2 na dukkan duniya sun shiga wannan aiki.

Ban da wannan kuma, a wannan muhimmiyar rana, wakilinmu ya sami labari daga ofishin jagorantar ayyukan gine-gine na gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 da cewa, bisa kididdigar da wannan ofis ya samu, an ce, a cikin dukkan filayen wasa guda 37 na gasar wasannin Olympic ta Beijing, ban da filin wasa na kasar Sin wato 'Shekar Tsuntsaye', an kammala gina dukkan sauran 36 lami lafiya. Za a kuma yi gwajinsu ta hanyar gasannin 'Fatan alheri a Beijing'. Kazalika kuma, za a fara aiki da filin wasa na Shekar Tsuntsaye a watan Afrilu na wannan shekara.

Ran 16 ga wata, an kaddamar da shirin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008. Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kaddamar da wutar yola da za a yi amfani da ita da fitilar wuta da sauran abubuwan da ke shafar aikin mika wutar yola. Wannan shiri na da sigar musamman a fannin kallo, ya sha bamban da na gasannin Olympic da aka yi a da, ya nuna al'adun gargajiya na kasar Sin sosai.

A kwanan baya, madam Deng Yaping, mataimakiyar shugaban sashen kula da kauyen 'yan wasan Olympic na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayyana a nan Beijing cewa, za a bude kauyen 'yan wasa masu shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing a ran 28 ga watan Yuli na wannan shekara, za a rufe shi a ran 27 ga watan Agusta. A lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, za a bude wa 'yan wasa nakasassu wannan kauyen 'yan wasa tun daga ran 30 ga watan Agusta zuwa ran 20 ga watan Satumba.

Ran 18 ga wata, a gun gasar gudun Marathon ta duniya da aka yi a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular Larabawa, shahararren dan wasa Haile Gebrselassie na kasar Habasha ya sami maki mai kyau da ya zama na biyu a tarihin gudun Marathon na maza, wato awoyi 2 da mintoci 4 da dakikoki 53. Wannan dan wasa ya taba samun maki mafi kyau a tarihin wannan wasa a shekarar bara.(Tasallah)