Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-30 19:23:27    
Tim din wasan tseren kwale-kwale na kwane-kwane na kasar Sin ya tattara fasahohi daga wajen gasar 'Good Luck Beijing'

cri
An yi budaddiyar gasar tseren kwale-kwale na kwane-kwane ta 'Good Luck Beijing' a wurin yawon shakatawa na ruwa na Olympic na Shunyi da ke Beijing tun daga ran 16 zuwa ran 19 ga wata. Tim din wasan tseren kwale-kwale na kwane-kwane na kasar Sin ya shiga gasar, yana fatan zai tattara nagartattun fasahohi daga wajen gasar don samun maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic na Beijing.

Ko da yake ita ba kasaitacciyar gasa ba ce, amma wannan budaddiyar gasar da kasar Sin ta shirya ta jawo dimbin nagartattun 'yan wasan kasa da kasa. Makasudin wadannan 'yan wasa gwanaye da su shiga wannan gasa shi ne domin wannan wurin yawon shakatawa na ruwa na Shunyi filin wasa ne inda za a yi gasannin tseren kwale-kwale na kwane-kwane a gun taron wasannin Olympic na Beijing. Shi ya sa sun zo nan domin dan taba wasan, ta yadda za su dace da wannan filin wasa, sun nemi share fage kan taron wasannin Olympic. A idanun malaman horas da wasanni da 'yan wasa masu yawa, ruwa na gangara cikin matukar sauri a hanyar ruwa da aka yi amfani a wannan karo, yawan ruwa ya yi yawa sosai, haka kuma, akwai babbar igiyar ruwa a ciki. A cikin dimbin hanyoyin ruwa da ake amfani a gun gasannin duniya, hanyar ruwa da ke Beijing na da sarkakkiya sosai. Shugaba Ulrich Feldhoff na hadaddiyar kungiyar tseren kwale-kwale ta kasa da kasa ya sifanta wannan hanyar ruwa da cewa,'Wannan hanyar ruwa na da sarkakkiya kwarai, yana kasancewa da bambancin zurfin ruwa mafi girma a cikinta, sa'an nan kuma, ana amfani da fasahar zamani wajen kafa ta. Yin takara a cikin wannan hanyar ruwa a gun taron wasannin Olympic zai iya bambanta mafi nagarta daga dukan 'yan wasa. Sai 'yan wasa mafiya kyau kawai za su iya sami maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic. Babu wanda zai taki sa'a zai ci nasara.'

Saboda sarkakkiyar wannan hanyar ruwa, 'yan wasa gwanaye masu yawa sun sha kaye a nan. Malam Andre Ehrenberg, malamin horas da wannin na tim din kasar Sin kuma dan kasar Jamus, ya ce,'Ita ce hanyar ruwa mai sarkakkiya ainun. Mun yi kwanaki da dama kawai muna aikin horo a nan, shi ya sa ba mu sarrafa gudanarwar ruwa a wannan hanyar ruwa sosai ba.'

Kamar yadda halin da 'yan wasa na sauran kasashe da yankunan duniya suke ciki, a karo na farko ne 'yan wasan kasar Sin sun yi gasa a wannan filin wasa. Babban gibin da ke tsakanin wadannan 'yan wasa matasa wajen yin gasa ya nuna abubuwan da aka gaza yi a fannonin fasaha da fasahohin yin gasa. Shugaba Li Xin na tim din kasar Sin ya yi nazari kan makin da tim din kasar Sin ya samu a wannan karo, ya ce,'A galibi dai, mun sami nasara, amma mun yi bakin ciki saboda wasu sun ci tura. Tim dinmu ya mai da hankali kan kananan gasanni 2, wato a tsakanin maza biyu biyu da kuma a tsakanin mace da mace. A gasar share fage ta tsakanin maza biyu biyu da aka yi a jiya, 'yan wasanmu suna da karfin samun lambar yabo, amma saboda su matasa ne, sun rasa samun fasahar yin gasa, ba su saki jiki ba, shi ya sa sun ci tura, ba su shiga gasa ta kusa da ta karshe a yau ba. Ban da wannan kuma, a cikin gasa ta tsakanin mace da mace, 'yar wasa Li Jingjing ta kasarmu ta nuna gwanintarta yadda ya kamata, ta yi fice sosai a gun gasar, amma tana fuskantar wasu matsaloli. A kofa ta 15, ta bata dakikoki 6 domin bace hanya. Inda ta kama hanya yadda ya kamata, watakila za ta zama zakara a yau.'

Game da matsalolin da suka bullo a wannan karo, malam Li ya kara da cewa,'Bayan da tim dinmu ya shiga wannan gasa, mun gano abubuwan kasawa, kamar su tunanin 'yan wasan da ke shiga gasa ta tsakanin maza biyu biyu, da akidar 'yan wasan da ke shiga gasa ta tsakanin mace da mace a fannin kama hanya, da kuma karfin jikunan 'yan wasa. Dukkan abubuwan da muka gano sun ba da taimako wajen kyautata aikin horo a nan gaba. Za mu rubanya kokarinmu wajen samun maki mai kyau a gun taron wsannin Olympic da za a yi a shekarar 2008 mai zuwa.'

Yanzu tim din kasar Sin yana da wata kungiyar malaman horas da wasanni masu kwarewa. Wannan kungiya sun hada da malaman horas da wasanni na kasar Jamus, wadda kasa ce mai karfi a wasan tseren kwale-kwale, da malaman horas da wasanni na kasar Sin da kuma malaman horas da wasanni na musamman masu nazarin kimiyyar wasanni. Kyakkyawan hadin gwiwar da ke tsakanin wadannan bangarori 3 ta taimaki tim din kasar Sin da ta kara samun kyakkyawan sakamako daga wajen aikin horo. Bayan da aka kammala wannan budaddiyar gasar kasar Sin, tim din kasar Sin za ta shiga gasar fid da gwani ta duniya a kasar Brazil, wadda take kasancewa wata dama daban gare shi wajen share fage kan taron wasannnin Olympic na Beijing.(Tasallah)