Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke jan akalar shirin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, yaran da suka sha nonon iyaye mata sun fi lafiya.
A cikin kwanakin nan da suka gabata, kwararru na kasar Rasha sun gano cewa, yaran da suka sha nonon iyayensu mata sun fi lafiya tun lokacin haihuwarsu har zuwa lokacin kuruciya idan an kwatanta su da yaran da ba su sha nonon iyayensu ba.
Kowa ya sani, shan nonon iyaye mata zai ba da taimako sosai ga yara, amma yanzu mata na kasar Rasha kadan daga cikinsu ne suke iya tsayawa kan shayar da yara nononsu. Kwararrun cibiyar binciken ilmin likita ta Kirov ta kasar Rasha sun yi wa yara 1238 bincike, kuma sun raba su cikin rukunoni biyu, daya shi ne rukunin shayar da yara nonon iyayensu mata, yaran da suka sha nonon iyayensu mata fiye da watanni tara sun shiga rukunin. Dayan kuwa shi ne rukunin da ba a shayar da yara nonon iyayensu mata ba, yaran da ba su sha nonon iyayensu mata ba da kuma wadanda lokacin da aka shayar da su nonon iyaye bai kai watanni uku ba sun shiga kungiyar.
Kwararru sun mayar da karfin garkuwar jiki da ya zama ma'aunin lafiyar yara. Daga baya kuma sun gano cewa, rukunin yara da aka shayar da nonon iyayensu mata ta nuna fiffiko a bayyane a lokacin haihuwarsu. A cikin shekara guda da aka haife su, yawan yaran da suka sha nonon iyayensu mata wadanda suka kamu da ciwon hanyar numfashi ya kai rabi idan an kwatanta shi da na daga rukunin daban. Amma kusan rabin yaran da ke cikin rukunin da ba a shayar da su nonon iyayensu mata ba sun kamu da ciwon hanyar numfashi har sau hudu a cikin shekara guda bayan haihuwarsu, kuma jariran da yawansu ya kai kashi 6 cikin dari sun kamu da ciwon huhu.
Bugu da kari kuma a lokacin kuruciya, yaran da ba su sha nonon iyayensu mata ba ba su da lafiyar jiki idan an kwatanta su da wadanda suka sha nonon iyaye mata. Yaran nan sun fi saukin kamuwa da ciwace-ciwacen hanyar numfashi da ciwon ciki.
To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gabatar muku wani labari daban kan cewa, maganin rage zafin haihuwa zai iya yin illa ga nonon iyaye mata. ani binciken da kasar Australia ta gudanar ba da jimawa ba ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne maganin rage zafin haihuwa zai yi illa ga nonon iyaye mata.
Bisa labarin da muka samu daga tashar Internetr ta mujallar "Sabbin masu ilmin kimiyya", an ce, manazarta na jami'ar Sydney ta kasar Australia sun gudanar da wani bincike ga mata 416 da aka yi musu allurar maganin rage zafin haihuwa lokacin da suke haihuwa da mata 312 da ba su sha irin wannan magani ba. Kuma sakamako ya gano cewa, game da matan da aka yi musu allurar maganin rage zafin haihuwa a cikin lakarsu da ke kashin baya, yiyuwar daina samar da nono lokacin da shekarun yaransu ya kai watanni shida ta ninka guda idan an kwatanta da wadanda ba su sha irin wannan magani ba.
Yin allura a cikin lakar da ke kashin baya tana daya daga cikin hanyoyin iri daban daban da a kan bi da ke wajen rage zafin haihuwa. Kuma manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba su gano cewa, ko maganin rage zafin haihuwa yana iya yin illa ga jarirai wajen shan nono, ko ga mata wajen samar da nono ba, shi ya sa ake bukatar ci gaba da yin nazari a kan shi.
Amma wani binciken da aka gudanar a da ya bayyana cewa, jariran da iyayensu mata suka sha maganin rage zafin haihuwa a lokacin haihuwa sun fi yawan barci idan an kwatanta su da wadanda iyayensu mata ba su sha maganin rage zafin haihuwa ba. Sabo da haka mai yiyuwa ne wannan zai iya yin illa ga jarirai wajen shan nono.
To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku shirin kuma ke cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)
|