Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-30 19:17:51    
Malam Shi Hu, kwararre a fannin zane-zane na kasar Sin

cri

A kwanakin baya ba da dadewa ba, an shirya wani nunin zane-zane a babban dakin nunin zane-zane na kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Wani zane na Malam Shi Hu, kwararre a fannin zane-zane na kasar Sin wanda aka nuna a gun wannan nunin ya jawo hankulan mutane kwarai.

A cikin wannan zanen, an nuna yadda marigayi shugaba Mao Zedong ke tadi da manoma cikin halin aminci. Da Malam Shi Hu ya tabo magana a kan wannan zane, sai ya ce, "a ganina, zamanin Mao Zedong zamani ne da ya fi faranta ran al'ummar kasar Sin. Sabili da haka na yi wannan zane ne don gwada juyin juya-hali da aka yi a zamanin yanzu a kasar Sin."

Malam Shi Hu mai shekaru 62 da haihuwa an haife shi ne a wani kauye mai suna "Chilu" na lardin Hebei da ke a arewacin kasar Sin. Babansa dan bako ne, kuma yana sha'awar rubuce-rubuce na wakokin gargajiya na kasar Sin ainun. Don haka tun lokacin da yake karami, sai babansa ya fara koya masa rubuce-rubuce na Sinanci. Amma yaro Shi Hu ya fi sha'awar zane-zane. Da shekarunsa suka kai 5 ko 6 da haihuwa, sai ya iya yin zane-zane masu kyaun gani a kan 'yan wasan kwaikwayo na gargajiyar kasar Sin.

Da shekarunsa suka kai 15 da haihuwa, an shigar da Shi Hu a cikin makarantar koyon zane-zane, a nan ne ya koyi aikin zane-zane da sassaka da sauran ayyukan fasaha na kasar Sin. Bayan da ya gama karatunsa a wannan makarantar, sai ya ci jarrabawar shiga Jami'ar Koyon Aikin Zane-Zane ta kasar Sin. Bayan shekaru uku wato yawan shekarunsa ya kai 18 da haihuwa, wani abin sassaka da ya nuna a gun wani nunin kayayyakin sassaka da aka shirya a birnin Beijing ya sami karbuwa sosai daga wajen 'yan kallo.

A shekarar 1978, Malam Shi Hu ya zama daya daga cikin 'yan kungiyar wakilan gwamnatin kasar Sin da suka yi ziyara a nahiyar Afrika. A wannan gami, ya shafe watanni uku da wani abu yana ziyarce-ziyarce a kasar Morocco, da Maritaniya da New Guinea da Kongo da kuma sauran kasashen Afrika ta arewa da ta yamma da kuma ta tsakiya. Halaye nagartattu na jama'a da kyawawan abubuwa da ya gani a nahiyar Afrika sun burge shi kwarai. Sai nan da nan ya yi zane-zane a kan wadannan abubuwa. Bayan shekara 1 da ya gama ziyara a Afrika, ya wallafa wani littafin zane-zanensa kan Afrika wanda ya ba bangaren zane-zane na kasar Sin mamaki kwarai, kuma ya sami karbuwa sosai daga wajen masu sha'awar zane-zane. Ya zuwa yanzu dai, Malam Shi Hu yana tunawa da wannan ziyararsa kamar abin ya faru ne a yau. Ya bayyana cewa, "ina sha'awar Afrikawa ainun. Haka nan kuma zane-zane da na yi a kansu da sauri, su ma sun ba su mamaki kwarai."

Ko da yake malam Shi Hu ya sami sakamako mai kyau wajen wallafa littafin zane-zanensa a kan Afrika, amma bai ishe shi ba. Sabili da haka ya sha yin tafiye-tafiye zuwa wurare dabam daban na lardin Henan da na arewacin lardin Shaanxi na kasar Sin don yin nazarin hanyoyi da ake bi wajen yin zane-zane na gargajiyar kasar Sin. Sa'an nan kuma ya koyi hanyoyi da ake bi wajen yin zane-zanen zamani na Turai. Daga baya dai ya kware wajen yin zane-zane cikin hadin guiwar fasahar Sin da ta Turai. Dangane da hakan ya bayyana cewa, " a hakika dai ya kasance da tsarin zane-zane iri biyu, wadanda suka hada da gargajiyar kasar Sin da na zamani na Turai. Ko da yake mun yi shekaru fiye da goma muna yin nazari a kansu, amma yayin da muke yin zane-zane, ya kamata, mu bi hanyar gargajiyarmu. "

A shekarun 1980, malam Shi Hu ya riga ya sami babbar nasara wajen shirya nunin zane-zane mai yawa a kasar Sin. Haka nan kuma ya sami karbuwa daga wajen bangarorin zane-zane na kasashen waje. A halin yanzu, yana rike da mukamin shugaban kungiyar Sinawa kwararru a fannin zane-zane ta duniya. Kungiyar nan ta kan shirya taron kara wa juna sani da nune-nunen kayayyakin fasaha da sauransu don yadada al'adun gargajiya ta al'ummar kasar Sin, da kara yin musaye-musayen al'adu a tsakanin kasa da kasa. (Halilu)