Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-29 21:25:40    
Gidan ibada mai tsarki a kafar manyan tsaunukan Helanshan

cri

A kafar manyan tsaunukan Helanshen a jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta da ke arewancin kasar Sin, a tsakanin manyan tsaunuka da koren itatuwa, akwai wani gidan ibada na addinin Buddha irin na Tibet mai dogon tarihi, wato gidan ibada na Guangzongsi.

Gidan ibada na Guangzongsi yana cikin yankin Alashan na jihar Mongolia ta Gida, yana kafar manyan tsaunukan Helanshan a yamma. Mazaunan wurin su kan kira shi gidan ibada na kudu, ko kuma gidan ibada na Nansi. An gina wannan gidan ibada bisa manyan tsaunukan. A kewayensa aka dasa dimbin itatuwa da ciyayi da kuma kyawawan furanni. Ana kuma iya jin kukan tsuntsaye a gandun daji. Wani lama mai suna Wuliji ya fita daga gidan ibadan domin maraba da mu. Wannan lama ya yi shekaru kusan 30 yana zama a gidan ibada na Guangzongsi. Yana koshin dukkan abubuwa a wannan gidan ibada. Wuliji ya yi mana bayani kan gine-ginen da ke cikin wannan gidan ibada. Ya ce,'Wannan gidan ibada ya hada da zauruka manya da kanana fiye da 20. Ban da wannan kuma, a babban zauren Dajingtang, ana ajiye mutum-mutumin na Sakyamuni da Zongkaba da masu koyonsa domin nuna girmamawa.'

An gina gidan ibada na Guangzongsi a shekarar 1758. Saboda an gina shi ne bisa manyan tsaunuka, shi ya sa mutum-mutumin Buddha masu launuka da aka sassaka a jikin manyan tsaunukan a bangarori 2 nasa suke da kyan gani kwarai.

A yayin da muka shiga gidan ibada na Guangzongsi, ana yi aikin karanta littattafan addinin Buddha irin na Tibet a ciki. A tsakanin laman da suke karantawa, ko tsoffi ko matasa, ta fuskokinsu ne muka iya gane cewa, dukkansu suna bin addinin da zuciya daya.

Ana ajiye gawar Dalai na 6 wato Cangyangjiacuo a gidan ibada na Guangzongsi domin nuna masa girmamawa, shi ya sa a zukatan mazaunan wurin, wannan gidan ibada shi ne wani wuri mai matukar tsarki. Suyilatu, mataimakin mai kula da gidan ibada na Guangzongsi ya gaya mana cewa,'Gidan ibadanmu na Nansi ya fi shahara a yammacin jihar Mangolia ta Gida, haka kuma, ana fi girmama shi. Saboda yana da nasaba da Dalai na 6 wato Cangyangjiacuo, wanda shi ne shugaban addinin Buddha a jihar Tibet mai cin gashin kanta.'

Ya zuwa yanzu dai, ana ajiye wasu kayayyakin tarihi masu daraja, kamar su littattafan addini da takardun bayanai da aka nannade da sauran abubuwan da Cangyangjiacuo ya taba amfani da su a gidan ibada na Guangzongsi.

Shen Sen da ya zo daga kudu maso yammacin kasar Sin ya bayyana mana ra'ayinsa game da kyan karkara na gidan ibada na Guangzongsi da kuma tarihinsa na addinin Buddha.

'Na taba ziyarar gidan ibada na Dazhaosi a jihar Tibet. Yau na yi farin ciki domin ziyarar gidan ibada na Guangzongsi a yankin Alashan. Na sami dama mai daraja ta kawo ziyara a wuri mai nisa kamar hakan. Watakila saboda ina koyon ilmin tarihi, ina sha'awar al'adun wannan gidan ibada kwarai. An yi tsit a wajen. An hada kyan karkara na muhalli da al'adun addini da kyau. Ina son in daukar hotuna da yawa, in nuna wa abokaina. Ban da wannan kuma, na zo nan tare da injin DV domin daukar hotuna kan kyan karkara.'

A shekarun baya, saboda goyon baya daga hukumar wurin, ana kiyayewa da bunkasa tarihin addini na gidan ibada na Guangzongsi da kuma al'adunsa yadda ya kamata, ana kuma girmamawa ikon mazaunan wurin wajen bin addini cikin 'yancin kai. Gao Jianzhong, mataimakin shugaban hukumar harkokin addini da kabilu ta shiyyar hagu ta yankin Alasha ya ce, 'Hukumar wurin na mai da hankali sosai kan harkokin kabilu da addini. Ta ba da kudin alawas ga lama masu nazarin addinin Buddha irin na Tibet. An shigar da wasu 37 a cikin tsarin ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta, ta haka an warware matsalolinsu a fannin zaman rayuwa, ba za su dami makomarsu ba.'

A lokacin da ake yawo a gidan ibada na Guangzongsi, laman suna tsabta gidan ibadanmu, suna kuma karanta littattafan addini, masu yawon shakatawa kuwa suna gurfana a gaban mutum-mutumin Buddha domin nuna girmamawa.

A kan bangon dutse da ke kusa da wannan gidan ibada, an rufe shi da kyallen da aka kira Hada masu launin shudi. Mutane sun yi iyakacin kokarinsu wajen jefa wadannan kyalle a sama domin neman samun sa'a.

Mutane sun bari farin cikinsu da dariyarsu a gidan ibada na Guangzongsi, sun kuma ajiye fatan alheri mafi kyau a zukatansu.