Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-29 17:41:26    
Kabaran sarakuna na daular Xixia

cri

Yau ran 24 ga wata, na kai ziyara a kabaran sarakuna na daular Xixia. Kabaran sarakuna na daular Xixia suna gindin dutsen Helan da ke yammacin birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia mai ikon tafiyar da harkokin kanta. An bine sarakuna 9 na daular Xixia a wannan yanki mai fadin muraba'in kilomita fiye da 50.

Da na isa wannan yanki na kabaran sarakuna, na kai ziyara a wurare uku, wato su ne, dakin da ke nune nunen kayayyakin tarihi na daular Xixia, da dakin nuna zane zane na sarakunan daular, da kuma kabaran sarakuna.

A cikin dakin da ke nune nunen kayayyakin tarihi na daular Xixia, na ga tsofaffin abubuwa da yawa, wasu sun bayyana kyawawan al'adu na wannan daula, wasu sun bayyana tattalin arziki na daular Xiaxia. Sabo da haka ne, na fahimta sosai, lallai, daular Xixia tana da daddaden tarihi.

A cikin dakin nuna zane zane na sarakunan daular, na ga yadda sarakuna suke mulkin kasa a zamanin da, ban da wannan kuma, na ga yadda farar hula suke zama a da. Zane zanen kuma sun ba ni wasu tatsuniyoyi masu ban sha'awa, wadanda aka gada daga zuriya zuwa zuriya.

Abin da suka fi ba ni sha'awa su ne kabaran sarakuna. Wadannan kabaran sarakuna suna da girma, a bayansu shi ne dutsen Helan. Dutsen Helan da wadannan kabaran sarakuna dukkansu suna da girma, karami sosai nake yi a gabansu. An ce, kabaran sarakuna na daular Xiaxia sun yi kamar Pyramid na kasar Massar. Hake ne, sabo da dukkansu suna da girma sosai, kuma an bine sarakuna na zamanin da a cikinsu.(Danladi)