Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-29 17:33:38    
Dakin wasa na birnin Beijing

cri

Masu karatu, bari mu ci gaba da ziyararmu a nan Beijing, inda za a shirya gasar wasannin Olympic ta karo na 29 a shekarar da muke ciki. Za mu yi muku gajeren bayani kan dakin wasa da za a yi shirin wasan kwallon raga ta gasar wasannin Olympic, wato dakin wasa na Beijing.

Dakin wasa na Beijing yana cikin yammacin birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, yana kuma makwabtaka da gidan zu na Beijing a gabas. Muhallin da ke kewayensa na da kyau sosai.

Wannan dakin wasa ya kafu a shekarar 1968, shi ne daya daga cikin manyan gine-gine guda 10 da suka yi suna a nan Beijing a shekaru 1960. Siffarsa ta yi kama da wani abu mai kusurwa 4, fadinsa ya kai misalin kadada 7, ya iya karbar 'yan kallo dubu 18. Dakin wasa na Beijing na matsayin daya daga cikin manyan dakunan wasa a kasar Sin, inda aka iya yi gasanni iri daban daban, haka kuma shi kadai ne dakin wasa a nan Beijing, inda aka iya yin gasar wasan kwallon gora a kan kankara. An iya tube benen katako da aka shimfida a cikin wannan dakin wasa. Bayan da aka tube su, benen dutse ya bullo. Bayan da aka zuba ruwa kan benen dutsen, bututun sanyayawa da aka ajiye a cikin benen dutsen sun fara sanyaya ruwan, har ma ruwan ya zama kankara. Saboda haka a ko wane lokaci na wata shekara, an iya samun kankara. Ko a lokaci mafi zafi, mutane sun iya kallon gasar wasan kwallon gora a kan kankara da kuma gasannin wasan kankara iri daban daban a cikin dakin wasa na Beijing.

A matsayinsa na wani tsohon dakin wasa mai tsawon shekaru kusan 40, an yi kwaskwarima kan dakin wasa na Beijing da kuma fadada shi, an kuma sabunta injunansa domin tabbatar da ma'auni wajen shirya shirin wasan kwallon raga na gasar wasannin Olympic ta Beijing. Abun da aka fi dora muhimmanci a harkokin kwaskwarima shi ne kyautata ba da haske a dakin wasan. A da an ajiye fitilu a rufin dakin wasan bisa tsarin rarraba taurari a sararin sama, wato a sama da wurin yin gasa, an ajiye jerin kwayayen fitilu masu ba da rawayen haske yadda ya kamata. In 'yan kallo suka daga kansu su duba sama, sai ka ce wadannan kwayayen fitilu sun yi kama da dimbin taurari da ke bullowar a sararin sama. Fitilun da aka ajiye bisa irin wannan tsari suna da matukar kyaun gani, kuma suna iya ba da haske yadda ya kamata, har ma sai ka ce hasken na iya dumama daki da zukatan mutane.

Amma bisa ma'aunin dakin wasa na zamani, irin wannan tsohon tsari bai isa ba, hasken da fitilun suka samar da bai isa ba wajen shirya gasa. 'Yan wasa ba su iya nuna gwanintarsu yadda ya kamata ba a karkashin irin wannan haske. Shi ya sa masu zayyana sun sha yin dabara. A karshe dai, sun fito da wani sabon tsari. Sun ci gaba da yin amfani da fitilu guda 220 da suka ba da haske kai tsaye daga rufin dakin wasan, sa'an nan kuma, sun kara kaddamar da wasu 132 a kawayen dakin wasan. Ta haka dukkan fitilun suna iya ba da isasshen haske, haka kuma, suna da kyaun gani sosai a idanun 'yan kallo