Jama'a masu sauraro. Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na Afirka a yau. A cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani dangane da matsalar rashin wutar lantarki a kasashen da yawa da ke kudancin Afirka
Ran 21 ga wata da dare, an sake samun matsalar rashin wutar lantarki a kasashen da yawa da ke kudancin Afirka. Kasashen Zambia da Zimbabwe sun sake samun matsala wajen samar da wutar lantarki bayan da aka gamu da irin wannan matsala kwanaki biyu da suka wuce. A Table Mountain wurin yawon shakatawa da ya yi suna da ke Capetown na kasar Afirka ta kudu, gugar da ke jawo mutane zuwa sama domin yawon shakatawa ba su iya tafiya saboda matsalar rashin wutar lantarki, masu yawon shakatawa darurruka ba su iya sauka daga dutsen Tabel Mountain.
A cikin shekarun baya, saboda bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, yankunan kasashen da ke kudancin Afirka suna bukatar makamashi, musamman ma wutar lantarki, a sakamakon haka, an samun matsalar karancin wutar lantarki a kasashe dabam daban, musamman ma a kasar Zimbabwe. Tun watan Yuni na shekarar 2007, kasar Zimbabwe ta fara tafiyar da manufar kayyade yawan wutar lantarki da ake yin amfani da su. Tun watan Yuni zuwa watan Agusta, an daina samar da wutar lantarki har awoyi 20 a yawancin yankunan kasar domin ba da tabbaci ga aikin gona. Kafin bikin Christmas da ya gabata, mazauna birnin Harare babban birnin kasar sun sha wahalar matsalar rashin wutar lantarki na tsawon lokacin da ya kai rabin wata domin ba da cikakken wutar lantarki ga masana'antu. Tun ran 19 zuwa ran 21 ga wannan wata, an samu matsalar rashin wutar lantarki wajen sadarwa, da zirga-zirga, da samar da ruwa, da asibitu, da tashoshin TV, wannan ya kawo mummunan tasiri ga zaman rayuwar kasar. Mr. Lafimo direkatan ofishin samar da wutar lantarki na kasar Zimbabwe ya nuna cewa, yanzu ana binciken dalilin da ya haddasa wannan matsala.
Tare da karuwar farashin jan karfe a cikin shekarun baya, kasar Zambia wadda ke da yawan albarkatun jan karfe tana bukatar wutar lantarki mai yawa. Matsalar rashin wutar lantarki da ta faru a ran 19 ga wata da dare ta sa masu hakan ma'adinai fiye da 400 su tsaya a karkashin rijiyar haka ma'adinai, har zuwa ran 20 ga wata da dare, an ceto su bayan da kasar Zambia ta jawo karfin wutar lantarki daga kasar Kongo Kinshasa. Direkatan ofishin samar da wutar lantarki na kasar Zambia, ya ce, irin wannan matsalar rashin wutar lantarki ba za ta faru ba a nan gaba, amma a sa'i daya, ran 21 ga wata da dare, matsalar rashin wutar lantarki ta sake faruwa a duk kasar, kuma an sake samun wutar lantarki har zuwa ran 22 ga wata da yamma.
Kasar Afirka ta kudu wadda ta zama kasa mafi cigaban masana'antu a kudancin Afirka ta kan samu matsalolin rashin wutar lantarki a shekarun baya. Bisa kididdigar da aka yi, matsalolin rashin wutar lantarki da su kan faru a kudancin Afirka sun riga sun haddasa hasara mai tsanani, a kasar Afirka ta kudu kawai hasarar ta kai ta dolar Amurka miliyan 280.
Kasashe dabam daban suna daukar matakai domin warware matsalar karancin wutar lantarki. Majaliasr dokoki ta kasar Afirka ta kudu ta fara kokarin gabatar da kudi ga kamfanin samar da wutar lantarki. Kakakin gwamnati ya nuna cewa, za a gabatar da shirin warware wannan matsala a cikin kwanaki masu zuwa. Ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin kasar za ta mai da aikin warware matsalar karancin wutar lantarki ya zama aiki mafi muhimmanci, da kafa shirin makamashi na dogon lokaci.
Ban da haka kuma, saboda kasar Afirka ta kudu ta daina samar da wutar lantarki ga kasashen da ke makwabtaka da ita, kasashen da ke makwabtaka da ita sun samun matsalar karancin wutar lantarki, bi da bi ne sun nemi sabon abokantaka domin warware wannan matsala. Kasar Swaziland da kasar Botswana sun neman taimaka daga kasar Mozambique. Kuma kasashen Zimbabwe da Namibia sun hada kansu domin samar da wutar lantarki. Kasar Zambia ta fara shigo da wutar lantarki daga kasar Kongo Kinshasa. A sa'i daya kuma, kwararrun kasar Sin sun je kasashen Zambia da Zimbabwe domin kara karfinsu wajen samar da wutar lantarki.
|