Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-29 12:43:40    
Ana gudanar da aikin gina filaye da dakunan wasannin Olympic lami lafiya

cri

Ran 28 ga wata, babban direktan hukumar ba da jagoranci ga ayyukan gine-gine ta shekarar 2008 ta birnin Beijing Mr.Chen Gang ya bayyana cewa, don biyan bukatun shiryan wasannin Olympic na 29, birnin Beijing yana bukatar gina filaye da dakuna 31, tare da dakunan horaswa 45. Ya zuwa yanzu, ban da babban filin wasannin motsa jiki da aka yi kusan kammalawa, sauran dakuna da filaye 30, an riga an gama dukkan ayyukansu, haka kuma an riga an gama aikin gina dakunan horaswa 44.


Mr.Chen Gang ya nuna cewa, birnin Beijing ya cika alkawarinsa na shirya wasannin Olympic ba tare da almubazaranci ba. Dukkan yawan jarin da aka zuba wajen gina dakuna da filaye 31, bai zarce Yuan biliyan 13 ba.(Bako)