Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-28 21:08:03    
Wasu labarai na kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya wakilinmu ya samu labari daga wajen sassan kiyaye kayayyakin tarihi na jihar Tibet ta kasar Sin cewa, kafin shekarar 2010, jihar Tibet za ta ware kudin Sin fiye da Yuan miliyan 100 domin kyautatawa da yin gyare-gyare ga wurin ibadan Tashilhunpo, duk kudin nan zai zo ne daga aljihun gwamnatin tsakiya.

An ce, wurin ibadan Tashilhunpo yana daya daga cikin gidajen ibada mafi shahara na addinin Buddha na Tibet, sabo da da dadewa ga ginawarsa, shi yasa yanzu wasu gidaje na wannan ibada ya lalace.

Bisa wani labari daban da aka bayar an ce, cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, yawan gidajen ibada da ni'imtattun wuraren ban sha'awa na tarihi da wurare masu yin bukukuwan addinai da aka kyautata kuma aka bude su a jihar Tibet ya kai fiye 1,400, don haka an ba da kariya mai amfani kuma cikin lokaci ga wadannan muhimman gine-ginen tarihi.

---- A ran 3 ga wata, an yi bikin bude tashar kwastan da ke arewacin iyakar kasa na ChuEnga Darboux a duk shekara, wannan ya zama hanya ta 3 ke nan da aka shimfida daga jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin zuwa kasashen Turai da Asiya.

An ce, tashar kwastan ta ChuEnga Darboux ta zama cibiyar tafiye-tafiye da ta hada wurare daban-daban na cikin kasar Sin, har da wasu larduna na kasar Mongoliya. Tun daga shekarar 2004 zuwa yanzu, tashar kwastan ta ChuEnga Darboux ta kara bude kofarta ga kasashen waje a duk shekara, kuma ta ware kudin Sin wato fiye da Yuan miliyan 200 domin shimfida hanyoyin mota da yin muhimmin gine-gine na tashar. Yanzu tashar ta riga ta samu sharudan tafiyar da harkokinta da yin zaman yau da kullum a duk shekara da shekaru.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta kara ware kudi da yawa domin kyautata muhallin halittu masu rai, sabo da haka aikin nan ya samun ingantuwa a jihar.

An ce, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet ta tsara kuma ta rubuta "shirin samun tabbaci wajen kiyaye da raya halittu masu rai na jihar Tibet", bisa wannan shiri da aka tsayar an ce, muhimman ayyukan da za a yi daga shekarar 2006 zuwa ta 2030 su ne ba da kariya ga shiyyoyin halittu da gandunan daji da filayen ciyayi da kuma kyautata su da sauran ayyuka fiye da 10. Yanzu ana nan ana gudanar da ayyuka na matakin farko yadda ya kamata, musamma ma daga ran 1 ga watan Janairu na wannan shekara, jihar Tibet ta fara aikin yin amfani da makamashi masu tsabta maimakon kiraren da ake amfani da shi yau da kullum, da kara rubanya kokari domin tsimin makamashi da raye yawan abubuwan kazanta da ake zubarwa, ta yadda za a raya zaman al'umma mai kyakkyawan muhalli.