Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-28 21:05:03    
Duniya na nuna amincewa ga ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki

cri

Ya zuwa karshen shekarar 2007, kasar Sin ta sami ci gaba mai faranta rai wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinta. Tun daga watan Janairu har zuwa watan Satumba da ya wuce, kasar Sin ta bunkasa harkokin tattalin arziki cikin sauri kuma kamar yadda ya kamata. Yawan kudin shiga da jama'ar birane da na kauyuka na kasar suka samu ya karu a bayyane, haka kuma kasar ta sami sabon ci gaba wajen tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, dukkan wadannan sun jawo hankulan gamayyar kasa da kasa sosai. Wasu 'yan siyasa na kasashe daban daban da jami'an hukumomin kasa da kasa da masanan ilmin tattalin arziki sun bayyana ra'ayoyinsu a kan tattalin arzikin kasar Sin.

A cikin farkon watanni 9 na shekarar bara, jimlar kudin da kasar Sin ta samu daga wajen samar da kayayyaki ta kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan dubu 16, wato ke nan ya karu da kashi 11.5 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2006. Mr Franz Jessen, mataimakin shugaban tawagar wakilan kungiyar tarayyar Turai a kasar Sin ya nuna babban yabo ga ci gaba da kasar Sin ta samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki cikin sauri sosai. Ya ce, "bisa manufar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar a shekarar 2000, an ce, yawan kudin da kasar ke samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP zai karu da ninki 1 a cikin shekaru 10 masu zuwa. Na yi imani cewa, bisa irin ci gaban da kasar Sin ke samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki cikin sauri, tabbas ne, gwamnatin kasar Sin za ta cim ma dukkan manufofin da ta tsara game da shirin shekaru biyar na raya kasa na 15."

Ya zuwa watan Disamba na bara, yawan kudin da jama'ar Sin suka kashe wajen sayan kayayyakin masarufi ya karu cikin sauri. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, tun daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar bara, matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane mazaunin birane da na garuruwa na kasar Sin ya samu ya karu da kashi 13.2 cikin dari, haka kuma matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane mazaunin kauyuka na kasar ya samu shi ma ya karu da kashi 14.8 cikin dari.

Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta kara kashe makudan kudade don kara jin dadin jama'a. Malam Vivek Arora, babban wakilin ofishin kungiyar ba da lamuni ta duniya ta IMF a kasar Sin ya bayyana cewa, "a ganina, wani abu mai faranta rai da ya faru a kasar Sin shi ne, gwamnatin kasar Sin ta kara kashe makudan kudade wajen samar da ilmi da aikin jiyya da kuma sauran fannonin zamantakewar al'umma. Wannan zai ba da taimako wajen daga matsayin zaman rayuwar jama'a, da bunkasa harkokin tattalin arzikin cikin daidaituwa daga manyan fannoni."

Kazalika tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka wajen kyautata tsarin tattalin arziki a manyan fannoni. Malam Rajendra Pachauri, shugaban kwamitin musamman mai kula da sauyawar yanayi a tsakanin gwamnatoci na majalisar dinkin duniya ya nuna yabo ga kasar Sin bisa kokarin da ta yi wajen yin amfani da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba, da kara daga matsayin yin amfani da makamashi. Ya ce, "kasar Sin tana kokari wajen yin amfani da hasken rana da karfin iska da sauran makamashi ba tare da gurbata muhalli ba. Sa'an nan kuma kasar tana kokari sosai wajen daga matsayin yin amfani da makamashi da rage yawan hayaki mai dumama yanayi da take fitarwa."

Masanan ilmin tattalin arziki na kasashen waje suna ganin cewa, kasar Sin ta riga ta ba da babban taimako ga duniya ta hanyar bunkasa harkokin tattalin arzikinta cikin sauri. Kuma suna sa ran alheri ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2008. (Halilu)