
A yau litinin ne aka kaddamar da cibiyar wasannin iyo da ninkaya ta Olympics, bayan tsawon shekaru hudu da aka dauka ana gina ta. Cibiyar wasannin na iyo da ninkaya, wadda kuma aka wa lakabi da ''Water Cube'' tana da wurin zama na mutune 17.000, kuma za a yi amfani da ita ne a lokacin gasar wasannin olympics na bana a nan birnin Beijing.
Tun daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa ran 5 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da gwajin amfani da kayayyakin wannan cibiya, a wata gasar zakaru a wasannin iyo da ninkaya.

Bugu da kari, an kayata ginin wannan cibiyar wasannin iyo da ninkaya, kuma ita ce cibiya mafi girma a duniya domin gudanar da wasannin cikin ruwa.
Ana sa ran sake yi wa wannan cibiya kwaskwarima bayan kammala wasannin olympics daga ranar 8 zuwa 24 ga watan Agusta. Daga bisani kuma za a maida ita cibiya ta musamman domin wasanni daban-daban. ( Yakasai )
|