Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-25 19:18:59    
Shugaban majalisar dattawa na Jamhuriyar Kazakhstan ya nuna fatan alheri ga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing

cri
A ran 25 ga wata, shugaban majalisar dattawa na Jamhuriyar Kazakhstan Kassymzhomart Tokaev da 'yan kungiyarsa da ke ziyara a kasar Sin, sun ziyarci makarantar koyon harsunan waje mai suna Qianmen ta Beijing, domin nuna fatan alheri ga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing.

Makarantar koyon harsunan waje mai suna Qianmen ta Beijing da makarantar koyon ilmin wasannin motsa jiki ta Almaty ta kasar Kazakhstan makarantu ne masu hadin kai kan wasannin Olympic. Tokaev ya kalli katakon nune-nune da dalibai suka yi game da kasar Kazakhstan a fannonin tarihi da al'adu da wasannin motsa jiki da dai sauransu. A cikin jawabinsa, ya ce, yana fatan daliban kasashen biyu za su iya kara yin cudanya kan al'adu da wasannin motsa jiki da dai sauran fannoni. Ban da wannan kuma, ya nuna fatan alheiri ga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing. (Zubairu)