Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-25 16:31:27    
Labari game da lardin Yunnan

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu a kullum wanda ya fito daga birnin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya. Kwanan baya, malamin ya turo mana wasikar da ke cewa, Yunnan shi ne lardi kwaya daya na kasar Sin da ke makwabtaka da kasar Laos, shin mutane nawa ne suke da zama a wannan lardi, kuma wane irin cigaba ne wannan lardi yake samu tun kafa shi, ko kunming yana daya daga cikin manyan birane na kasar Sin?

To, masu sauraro, domin amsa tambayoyin, yau bari in zagaya da ku wannan lardi na Yunnan

Kasancewar lardin Yunnan a kudu maso yammacin kasar Sin, yana iyaka da kasashen Myanmar da Laos da kuma Vietnam a waje da kuma lardunan Guizhou da Guangxi da Sichuan da kuma Tibet a gida. Fadin lardin Yunnan ya kai murabba'in kilomita dubu 394, wanda ya dau kashi 4.1% daga dukan fadin kasar Sin. Hedkwatar lardin Yunnan yana birnin Kunming, wanda ake masa kirari da birni ne na bazara, sabo da birnin, ba a zafi sosai a lokacin zafi, kuma ba a sanyi sosai a lokacin dari.

Yunnan ya yi suna ne da abubuwa da yawa. Na farko shi ne yanayin kasa. A lardin Yunnan, ana samun ruwan sama sosai a duk shekara, kuma akwai dimbin koguna da tabkoki a cikin lardin, ciki har da koguna manya da kanana fiye da 600, tare kuma da tabkoki 37 da fadinsu ya wuce muraba'in kilomita 1. Sa'an nan kuma, a lardin Yunnan, akwai kyawawan tsaunuka masu yawa. Sabo da kyakkyawan yanayin kasarsa, lardin Yunnan ya shahara sosai a wajen yawon shakatawa.

Bayan haka, lardin Yunnan yana kuma wadace da albarkatun kasa iri iri. Ciki har da ma'adinai 142 da aka rigaya aka gano da kuma dabbobi iri iri 1737 tare kuma da kwari da ire-irensu da suka wuce dubu 10. Bayan haka, lardin Yunnan yana kuma da arzikin makamashi, wadanda suka hada da na ruwa da na rana da na iska da na kasa, musamman ma makamashin ruwa, sabo da dimbin kogonan da yake da su.

A nan kasar Sin, gaba daya akwai kabilu 56, wato kabilar Han da kuma sauran kananan kabilu 55. daga cikin wadannan kananan kabilu 55 kuma, akwai 51 da ke zama a lardin Yunnan, sabo da haka, lardin Yunnan ya zama lardin da ya fi samun yawan kabilu a kasar Sin. A lardin Yunnan, kabilu daban daban suna zaman jituwa da juna da kuma hadin kai da juna. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, musamman ma bayan da Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, bisa kokarin da kabilu daban daban suka yi, lardin Yunnan ya sami saurin bunkasuwa a fannin tattalin arziki da kuma harkokin zaman al'umma, kuma manyan ayyukan makamashi da sadarwa da kuma sufuri ma sun kyautata. Kasancewar lardin Yunnan a kan iyakar kudu maso yammacin kasar Sin, Yunnan ya sami cigaba cikin sauri a wajen ciniki da kasashen waje, kuma kofarsa a bude take ga kudu maso gabashin Asiya da kuma duniya baki daya. Tun daga shekarar 1993, lardin Yunnan ya hada kansa da sauran lardunan kudu maso yammacin kasar Sin, har ma sau shida ne suka cimma nasarar gudanar da bikin baje kolin kayayyakin fici na birnin Kunming na kasar Sin, yanzu Yunnan na kara zama kofar kudu maso yammacin kasar Sin ga waje.

Masu sauraro, idan kun sami damar zuwa kasar Sin a wata rana, kada dai ku wuce lardin Yunnan.(Lubabatu)