Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-25 15:48:55    
Kasar Kenya ta taka wani mataki mai muhimmanci wajen warware matsalar siyasa

cri

Ran 24 ga wata da yamma, a karkashin shugabancin Mr. Kofi Annan tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya, Mr. Kibaki shugaban kasar Kenya da Mr. Odinga shugaban jam'iyyar ODM mai adawa snn yi shawarwari tare a birnin Nairobi. Bangarorin biyu na kasar Kenya sun taka wani mataki mai muhimmanci wajen kawo karshen halin kaka-ni-ka-yi da kuma warware matsalar siyasa. To, yanzu sai ku saurari rahoton da wakilnmu Xie Yi ya aiko masa daga kasar Kenya.

Bayan shawarwarin da suka yi, bi da bi ne Mr. Kibaki da Mr. Odinga suke bayar da jawabi. Mr. Odinga ya nuna cewa, bangarorin biyu sun riga sun sami ra'ayi iri daya wajen neman warware matsalar siyasa ta hanyar shawarwari. Ya ce, "Yau na yi shawarwari tare da Mr. Kibaki, kuma za mu cigaba da yin shawarwari har mu warware matsalar da muke fuskanta."

Mr. Kibaki ya yi alkawarin cigaba da yin shawarwari, kuma zai shugabancin jama'ar kasar Kenya domin neman hadin kai, da nuna hakuri, da zaman lafiya da kuma zaman jituwa. "Zan cigaba da kokarin yin shawarwari domin neman samun jituwar al'umma a dukkan fannoni. Muna kokarin hanyar warware matsalar siyasa da muke fuskanta. Kuma a wannan lokaci, na yi kira ga dukkan jama'ar kasar Kenya da su kwanta da hankulansu domin kawar da sake aukuwar rikice-rikice."

Wannan ne karo na farko da shugabannin biyu suka gana da juna tun bayan babban zaben da aka yi a ran 27 ga watan Disamba na shekarar 2007. amma tashe-tashen hankali da aka samun kan sakamakon babban zabe sun riga sun yi sanadiyar mutuwar mutane 600, kuma mutane fiye da dubu 260 sun zama 'yan gudun hijira. Ko da yake tsawon shawarwarin da shugabannin biyu suka yi ya kai rabin awa kawai, amma bayan wannan shawarwari, shugabannin biyu sun yi murmushi, tare da yin shawarwari da musafaha, wannan ya ba da damar shimfida yanayin zaman lafiya ga jama'ar kasar Kenya wadanda suka sha wahala har tsawon wata guda. Wani mutum ya ce, "shawarwarin da shugabannin biyu suka yi suna da ma'ana sosai, saboda wannan zai kawo karshen tashe-tashen hankali da ake ciki." Wata mace ta ce, mun yi maraba da shguabannin biyu suka yi shawarwari, kuma muna fatan za su cigaba da yi shawarwarin yadda ya kamata domin shimfida zaman lafiya.

Bi da bi ne kasashen duniya da kungiyar MDD, da kungiyar AU, da kungiyar EU, da kasashen Sin da Amurka suka yi kira ga bangarorin biyu da su warware sabanin ra'ayi ta hanyar shawarwari. Yanzu, Mr. Kofi Annan, tsohon babban sakataren MDD ya ci nasara wajen yin sulhu tsakanin Mr. Kibaki da Mr. Odinga. "Ina tsamani mun riga mun taka mataki na farko wajen warware matsala ta hanyar zaman lafiya, kuma iya ganin shugabannin bangarorin biyu suna nan, kuma sun jaddada cewa za su yi shawarwari domin warware wannan matsala wadda ta dau dogon lokaci cikin adalci."

Amma, Mr. Kibaki da Mr. Odinga ba su ce kome ba kan yadda za a warware wannan matsala a zahiri ba. Ban da haka kuma, bayan awoyi da dama da suka kammala shawarwarin, Mr. Odinga ya zargi Mr. Kibaki cewa yana so ya malattad da mukaminsa na shugaban kasar, to amma hakan zai bata kokarin da kasashen duniya suka yi. Za mu iya ganin cewa, nan gaba Mr. Kofi Annan zai fuskanci abubuwa da ba su da sauki wajen yin sulhu.